DARA TA CI GIDA: Ƴan sanda sun damke bokan da ake zargin yana hada wa ƴan IPOB siddabarun neman sa’a

0

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Imo Abutu Yaro ya bayyana cewa jami’an ƴan sanda sun kama wasu mutum tara da ake zargi da kai hari kan gidan Gwamnan Jihar Hope Uzodinma.

Bayan haka a cikin wannan sanarwar wanda kakakin rundunar ƴan sandan Bala Elkana, ya saka wa yannu a madadin kwamishinan ya ce Uzoamaka Ugoanyanwu mai shekara 40 yana haɗa wa mayaƙan Eastern Security Network (ESN), wato bangaren mayaƙan IPOB tsafe-tsafen da suke rataya idan za su fita aika-aika.

Elkana ya ƙara da cewa ƴan sanda sun yi nasarar kama su ne sakamakon wani dogon bincike da suka yi.

Kusan duk lokacin da aka yi nasarar kama su ko kashe su sai ka ga tarin layu rataye a jikin su.

Share.

game da Author