Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya gama shiri tsaf domin komawa jam’iyyar APC a ranar dimokradiyya, wato 12 ga Yuni.
Majiya mai karfi ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa duk a shirin canja shekar ne matawalle ya yi wancakali da duka kwamishinonin sa da manyan shugabannin hukumomin gwamnatin
Jihar, harda sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.
Majiya ta shaida mana cewa ba gama shiri tsaf domin canja sheka bane, ba a fadi yadda makomar tsohon gwamna zai kasance ba. An ya za su iya zama rumfa daya kuwa a jam’iyya daya, sannan kuma shugabancin jam’iyya dole ta tashi da ga hannun Abdulaziz Yari ta koma hannun gwamna Matawalle.
Matawale ya kori kwamoshinoni sa
A wata sanarwar da ta fito daga ofishin kakakin gwamnan, Bappa Zailani, ranar Talata, gwamna Matawalle ya umarci duka wani shugaban wata hukuma ta gwamnati a jihar ya mika ragamar shugabancin hukumar ga babban darekta a ma’aikatar sa.
Wannan kora bai bar kusan kowa ba domin ya faro ne tun daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnan jihar, zuwa sakataten gwamnatin jihar ya gangara har kwamishinoni sai kuma shugabannin ma’aikatun gwamnatin jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce kwamishina daya ne tal ne kawai ba a wancakalar ba, kwamishin Tsaro da Harkokin cikin gida, Mohammed Tsafe.
Discussion about this post