Dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ta dakatar da Tiwita a Najeriya – Lai Mohammed

0

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da ayyukan shafin Tiwita a Najeriya.

Wannan sanarwa na kunshe ne a wata takarda wanda ta fito daga ofishin ministan yada labarai, Lai Mohammed.

Lai Mohammed ya ce gwamnati ta dakatar da shafin tiwita a kasar nan ne saboda shafin na neman kawo rudani da wargaza hadin kai da tsaro a kasar.

Idan ba a manta ba, tiwita ta cire wani bangare na jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari a farkon wannan makon.

Wannan abu da kamfanin yayi ya samu suka daga yan Najeriya da suka yi ikirarin cewa ba a yi wa shugaban adalci ba, cire wadannan kalamai na sa da tiwita ya yi.

A wani martani da gwamnatin kasar ta maida wa tiwita, ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa alamu duk sun bayyana cewa akwai boyayyar ajanda da tiwita take dashi a Najeriya.

Lai Mohammed ya ce bai ga illar kalaman Buhari ba da tiwita zai cire a shafinsa.

Gwamnati ta zargi tiwita da ruru wutar tashin hankali a kasar nan ta hanyar masu adawa da gwamnati da neman tada zaune tsaye da kuma yin amfani da dandalin wajen cin karen su ba babbaka.

Tiwita har wata alama ta kirkiro da shi a lokacin da yan Najeriya ke zanga-zangar EndSars, domin mara musu baya.

Share.

game da Author