Cikin wani al’amari mai kamada barazana, an fara tilastawa iyayen daliban Jami’a mallakar Jihar Kaduna dasu sanya hannu kan wata takarda cewa ‘ya’yansu bazasu kara yin zangazangar kin amincewa da karin kudin makaranta ba, kuma idan sunyi za’a koresu daga makarantar.
A baya, daliban sunyi ta yin zangazangar kin amincewa da karin kudin makaranta domin tilastawa gwamnatin Jihar ta janye karin kudin da tayi domin baiwa dalibai masu rangwamen gata damar suyi karatu a jami’ar.
Gwamnatin Jihar tayi karin kudin makarantar har zuwa N300,000 da N400,000 mafi kololuwa akan abinda ake biya a baya na naira N36,000. Kacal.
Jami’ar ta fitar da takardar hana zangazangar ne ta ofishin rijistara, Samuel Manshop, inda tasa iyayen yara sanya hannu cewa dole ya’yansu suyi biyayya akan dokokin makarantar ko wacce irice.
A cikin takardar an rubuta cewa “ni mahaifin wane ina bada tabbacin cewa dana ko ‘ya ta zasu bi dokar makaranta kuma a koresu idan har sun karya dokar makarantar ta hanyar shiga wata zangazangar kin amincewa da karin kudin makaranta ko wani doka da makaranta ta kafa”.
Rijistara Manshop bai amsa wayar PREMIUM TIMES ba da sakon karta kwana a ranar Alhamis da Juma’a domin jin ta bakin makaranta akan takardar ta hana dalibai zangazangar neman hakkinsu.
Sai dai kuma jami’ar a shafinta shafinta na Facebook ta karyata cewa ta fitar da takardar hana zangazangar, amma bata yi Ƙarin bayani ba, haka shima, kwamishina tsaron jihar Samuel Aruwan ya saka cewa wannan takarda ba gaskiya bace.
Kafin karin kudin makarantar, dalibai yan asalin Jihar Kaduna na biyan kudi naira N24,000 da N26,000 bisa la’akari da bangaren da dalibi yake karatu.
Dalibai da ba yan Kaduna ba na biyan kudi naira N31,000 da 36,000, shima la’akari da bangaren da dalibi ko daliba ke karatu.
Bayin anyi kari dalibai yan Kaduna zasu fara biyan N150, 000 da kuma N171, 000 yan wasu jahohi kuma zasu biya N221,000.
A Shashen koyar da halayya Dan Adam wato social sciences, dalibai ‘yan asalin Jihar zasu biya N170,000 a inda sauran dalibai zasu biya N200,00.
Haka kuma, daliban Jami’ar da aka dauka domin suyi karatun likita zasu biya N300,000 sa’annan su kuma sauran dalibai zasu biya N400,000