Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta sake bude Tiwita idan kamfanin ya tabbatar wa kasar nan cewa ba zai rika watsa shiririta da soki-burutsun da zai haddasa fitina ba.
Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da wasu jakadun kasashe na nan Najeriya.
Ya ce duk da dai ba zai iya cewa ga ranar sake budewa ba, amma dai babban sharadi shi ne a matsayin Tiwita na soshiyal midiya, ta tabbatar ta kasance kafar yada abin alheri da alfanu, ba sharri ba.
“Matsawar aka ce ka na da karfin da za ka iya isar da sakonni, to ya kamata ka rika gudanar da wannan sana’a a cikin mutunci ba da cin zarafi ko kokarin haddasa fitina a kasa ba.” Haka Onyeama ya shaida wa manema labarai.
“Ba mu ce Tiwata na yi wa kasar nan wata barazana ba, a’a. Mun dakatar da saboda kawai sun bari ana amfani da su domin a kawo rudun da ka iya hargitsa kasa ko kafar aikata muggan laifuka.”
Ya ce abinda gwamnati ta zartas na daga cikin muhimman batutuwan da su ka shafi tsaron kasar nan.
“Saboda idan Babu tsaro, to duk gaba daya ne duk za mu yi asara.
Tuni dai kungiyar SERAP ta yi barazanar za ta ƙalubalanci Gwamnatin Buhari a kotu.
Kungiyar SERAP ta ce hana amfani da kafar soshiyal midiya ta twitter da Gwamnatin Shugaba Muhammadu ta yi, haramtacce ne, kuma ƙungiyar ta ce za ta gaggauta maka gwamnatin tarayya kotu.
SERAP ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter, ko kuma ta maka ta kotu kai-tsaye.
A ranar Juma’a ce Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana dakatar da twitter daga amfani a Najeriya har sai yadda hali ya yi.
Kaakin Yaɗa Labarai na Minista Lai, Segun Adeyemi ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin ministan.
Sai dai kuma jim kaɗan bayan fitar da sanarwar, SERAP a fusace ta kira dakatarwar haramtacciya, kamar yadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Olueadare ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
“Dakatar da twitter a Najeriya tauye wa ‘yan Najeriya ‘yancin faɗar albarkacin bakin su ne da kuma toshe masu wata muhimmiyar kafar samun bayanai da aika saƙonni.
“Wannan dakatarwar wani salo ne aka yi amfani da shi na azabtar da mutane bai-ɗaya a lokaci guda. Hakan ya saba wa tsarin dokokin ƙasa-da-ƙasa.
“Saboda haka mu na kira ga Shugaba Buhari ya gaggauta janye wannan dakatarwar, cikin sa’o’i 48 ko kuma mu da shi mu haɗu a kotu, saboda ya danne haƙƙin jama’a masu tarin yawa.
Discussion about this post