Daga yanzu duk mai watsa labarai a Najeriya ta yanar gizo ko Soshiyal Midiya sai yayi rajista da NBC

0

Hukumar NBC ta bada sanarwar cewa duk wani kamfanin yada labarai da shafukan Soshiyal Midiya a yanar gizo dake aiki a kasar nan ya garzaya ofishin hukumar domin yin rajista.

Sanarwar ta kara da yin gargaɗi ga duk masu sana’ar watsa labarai a yanar gizo dake ayyukan su a kasar nan da su tabbata sun yi rajista da hukumar, idan ko ba haka ba za a tuhume su da karya doka.

NBC ta ce doka ya ba hukumar damar tilasta masu kamfanoni da shafukan da ke watsa labarai kai koma ‘jagwalgwalo ne’ yin rajista dole kafin su yi aiki a kasar nan a bayyane ko kuma ta hanyar yanar gizo da Soshiyal Midiya.

Tun farko gwamnati ta bayyana a baya cewa za ta saka doka irin haka domin kawo karshen yadda wasu ke amfani da kafafen soshiyal midiya suna watsa labaran karairayi da na kanzon kurege domin tada zaune tsaye a kasar nan.

Sai dai kuma tun kafin hukumar ta fidda wannan sanarwa ƴan Najeriya sun yi ta yin tir da nuna rashin amicewar su ga shirin.

Da yawa na ganin yin hakan hance kawai na tauye wa mutane dama da dokar kasa ta ba su na fadin albarkacin bakin su game da koma menene a kasar nan.

Wannan sanarwa dai na nufin ba kowa bane zai kawai zai iya yin gaban kansa ya fara watsa labarai a yanar gizo yadda ya ga dama sai dole ya yi rajista kuma an bashi lasisin yin haka daga hukumar NBC.

Share.

game da Author