Jam’iyyar PDP mai adawa a Jihar Jigawa tace yan takaranta shida ne kawai cikin ashirin da bakwai zasu shiga zaben kananan hukumomi da za’a a gobe Asabar
Shugaban Jam’iyyar na PDP a Jigawa, Babandi Ibrahim, yace da gan gan hukumar zaben ta sa kudin siyan fom har N500,000 saboda tsoron cewa PDP zata lashe zaben idan har sunyi takara amma saboda halin yau Yan takaran PDP bazasu iya sayan fom domin yin takara ba.
Babandi ya ce PDP saboda rashin kudi zata shiga zaben ne kawai a kananan hukumomin, Dutse, Birnin Kudu, Hadejia, Kiyawa, Guri, da kirikassamma, yayi kira da yan kananan hukumomin dasu fito su zabe PDP su kunyata APC kamar yadda Yan Zaria suka yi a Kaduna domin cigaban Jihar Jigawa.
Munyi iya kukarinmu muga cewa hukumar zaben ta Jiha ta rage kudin fom amma tayi kunen uwar shegu ta siyar da fom akan kudi har naira N500,000 ga yan takarar ciyamomi sai kuma N200,000 kudin fom ga yan takarar kansiloli, inji Babandi.
Babandi ya kuma cewa anyi hakan ne domin tauyewa yan adawa hakkinsu na shiga zabe wanda kuma ya sabawa dokar kasa da tsarin mulki irin na demokaridiyya.
Anyi hakan ne kawai domin an san idan mun shiga zaben zamuyi nasara shi yasa akayi mana kora da hali, inji Babandi.
Premium Times Hausa tayi kokarin jin ta bakin Shugaban hukumar zaben na Jihar Jigawa, Adamu Ibrahim, ranar Talata, Laraba da Alhamis amma abin ya citura.
Amma mataimakin Gwamnan Jigawa, Usman Namadi, ya shaidawa yan Jaridu cewar anbawa yan adawa damar shiga zaben kuma za’ayiwa kowa adalci wajen yin zabe karbabbe kuma mai inganci.
Namadi yace Jam’iyyarsa ta APC ta kawo cigaba a Jihar Jigawa da kuma taimakawa talakawa fiye da duk wasu gwamnotoci da suka gabata, saboda haka yace abinda ya faru a zariya bazai faru a Jigawa ba.
Abinda ya faru a zariya alamu ne na cewa APC tana bin tsarin dimokaridiyya kuma dole a yaba mata saboda ta bar mutane sun zabi abinda suke so.
A Jigawa ma gwamna Muhammad Badaru ya bada umarnin ayi adalci ga kuwa wajen yin zabe mai inganci kuma duk wanda yaci abashi, inji malam Namadi.