Buhari ya shirya, zai miƙar da duk wani taƙadarin da ya karkace -Femi Adesina

0

Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya jaddada goyon bayan sa a kan zafafan kalaman da Shugaba Buhari ya yi a cikin wannan makon, wanda ya ja har aka twitter ya kulle shafin sa.

Cikin wani rubutu da Adesina ya yi, wanda aka wallafa a ranar Juma’a ɗin nan, Adesina ya nuna cewa Buhari ya yi daidai da ya ce zai yi amfani da ƙarfi ya dankwafe duk wani kangararre.

Wannan kakkausan kalami dai an fassara shi da cewa Buhari na magana ne a kan ‘yan kungiyar IPOB na jihohin Kudu maso Gabas, inda ake ci gaba da banka kadarorin gwamnati wuta, musamman ofisoshin INEC da na ‘yan sanda, tare kuma da kashe jami’an ‘yan sanda da dama.

Adesina ya ce Buhari ya yi mamakin yadda Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana masa cewa, “A cikin shekaru biyu an ƙona ofisoshin INEC har 42.”

A kan haka ne Adesina ya bayyana cewa, ya ji dadin yadda wani mai sharhi ya ce: “Jama’a Buhari ya bi ku da lalama, amma kun ce ba ya magance matsala sai iya daɗin-baki. Yanzu kuma ya ɗauko hanyar maganin marasa kunya kun zo ku na ta surutai. To ku na so ya yi tsaye ya na kallon ana ƙona dukiyar a ƙasa, a matsayin sa na Shugaban Kasa?”

Adesina ya ƙara da cewa Buhari ba zai saurara wa kowa ba.

“Abin da zai magance duk wata rashin kunya a ƙasar nan, shi ne a yi amfani da irin salon mulki mai TSANANI irin na BUHARI lokacin da ya yi MULKIN SOJA, duk kuwa da cewa mulkin DIMOKRAƊIYYA ne ake yi a yanzu. Ita dimokrɗiyya ba hauka ba ce. Duk wani wanda ya kangare ko a wane YANKIN ƘASAR nan ya ke, a yi ta zabga masa bulala har sai ya yi lilis. Shi da kan sa zai dawo kan miƙaƙƙar hanya!”

Har ila yau, Adesina ya tunatar wa ‘yan Najeriya cewa Buhari ba kanwar lasa ba ne, saboda a baya ya yi an gani, kuma ya bi da maza sun yi ladab.

“Buhari shugaba ne fa tamkar rodi. Don haka a yanzu ya shirya, har ya mulmula kulkin sa. Babu sauran jira ko jinkiri, zai riƙa kwankwatsar kan duk wani mai taurin kai.”

Adesina ya kuma bayyana cewa “duk wani masoyin Buhari na gaskiya, ya ji daɗin zafafan kalaman da Buhari ya yi, waɗanda Adesina ɗin ya ce amma ‘yan hauragiya ke ta surutai marasa kan-gado.

Share.

game da Author