Buhari ya ce daƙile rashawa da cin hanci abu ne mai wuya a tsarin dimokraɗiyya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kakkabe cin hanci da rashawa a ƙarƙashin mulkin ɗimokradiyya abu ne mai matukar wahalar gaske.

Ya yi wannan furuci cikin wata tattaunawa da Gidan Talbijin na Arise TV ta yi da shi a ranar Alhamis.

Ya ce tun da ya hau mulki cikin 2015, ya ke ta gaganiya kan yaki da rashawa da cin hanci kuma yakin ba abu ba ne mai sauki.

Sai dai kuma ya bugi kirjin cewa gwamnatin sa ta yi gagarimar nasarar hankaɗe jami’ai da shugabanni masu wuru-wuru ba tare da ta rika yayatawa ba.

“Idan kun tuna ai na yi nasarar korar rashawa a zamanin da na yi mulkin soja, kafin a kifar da gwamnati na.”

Buhari ya nuna bacin rai ganin yadda ake tafiyar da kananan hukumomi a kasar nan. Ya kara da cewa a yanzu tamkar ma babu tsarin kananan hukumomi zai iya cewa.

“Wane irin mulki ne a ce an bai wa karamar hukuma naira milyan 300, amma gwamna ya danne, ya ba ta naira miliyan 100 kacal? Akwai rashin adalci a lamarin.” Inji Buhari.

A kan ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, Buhari ya ce ai ya bayar da umarnin cewa kada jami’an tsaro su rangwanta masu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake shan alwashin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da kuma rikicin Fulani makiyaya da manoma.

Cikin wata tattaunawar da Gidan Talbijin na Arise TV ya yi da Buhari, Shugaban Kasa ya ce gwamnatin sa ta yunkuro wajen samar wa Fulani makiyaya burtali da wurin kiwo.

Sai dai kuma Buhari bai maida hankali wajen mafita kan ‘yan bindiga masu garkuwa da daruruwan ‘yan makaranta ba.

Har yanzu ‘yan bindiga na ci gaba da ragargazar kauyuka da garuruwan Arewa, inda ta kai ga yanzu sun kai ga kutsawa Jihar Kebbi su na mummunan kisa, kamar irin yadda su ke yi a Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja.

Da ya koma kan Boko Haram, Buhari ya ce “Yunwa, Talauci da Rashin Aiki ga Matasa ke Haddasa Boko Haram.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yunwa, talauci da rashin aikin yi ga matasa ne su ka haddasa Boko Haram kuma su ke kara ruruta wutar ta’addanci.

Haka Buhari ya bayyana a tattaunawar musamman da ya yi da Gidan Talbijin na Arise TV, ranar Alhamis, a Abuja.

“Na yi amanna gwamnati na ta yi kokari tukuru wajen yaki da Boko Haram, amma matsalar da ake ciki a yankin Arewa maso Gabas abu ne mai wuyar sha’ani.”

Ya ce ya hakakke cewa mafi yawan ‘yan Boko Haram, ‘yan Najeriya ne, kamar yadda Gwamnan Barno, Babagana Zulum ya shaida masa.

Sai dai kuma Buhari bai yi magana kan yadda malaman addini su ka assasa Boko Haram ba, ta hanyar amfani da wasu litattafan magabatan malamai, ta yadda Boko Haram sun yarda su jihadi su ke yi bil-hakki da gaskiya.

Share.

game da Author