Maimartaba Shehun Barno, Abubakar Elkanemi, ya bayyana wa babban hafsan sojojin Najeriya, janar Farouk Yahaya cewa har yanzu fa akwai garuruwa da hanyoyin da mutum bai isa ya je su ko ya bi ba, idan ma ya bi to fa zai bi da alwalarsa ne domin zai iya yayi sallama kenan da duniya saboda Boko Haram.
Shehun ya kara da cew duk da an samu dimbin nasarori a yaki da Boko Haram da gwamnati ke yi, har yanzu akwai sauran aiki a gaban sojojin Najeriya.
” Kafin zuwan gwamnatin Buhari a 2015, akwai akalla kananan hukumomi 17 da jama’ suka yi sallama sa su kwata-kwata saboda mamaye su da Boko Haram suka yi, amma ina tabbatar maka cewa yanzu babu karamar hukuma ko daya dake karkashin ikon Boko Haram.
” A baya fa ya kai ga hatta asibiti, makarantu, hanyoyin sadarwa duk ba su aiki, amma yanzu an samu canji matuka. Sai dai muna rokon a ci gaba da ma maida hankali akai domin mutanen mu su samu su koma gonakin su.
” Mutanen jihar Barno manoma da masunta ne, rashin komawa gonaki da sauran sana’o’in su yana kawo mana cikas matuka. Boko Haram sun tsare wuraren, manoma ba su iya kaiwa ga gonakin su.
Jerin garuruwa da hanyoyin da Boko Haram ke kai hare-hare har yanzu
1 – Baga, Krenoa, Marte Gamboru-Ngala dake da iyaka da tafkin Chadi
2 – Hanyar Maiduguri – Damboa
3 – Gubio – Damasak
4 – Magukeri – Damasak
5 – Maiduguri – Monguno
6 – Brimari da Gasara
7 – Damboa-Biu
8 – Malumfatori
9 – Gudumbali
10 – Dikwa-Ngala
A jawabin sa, Janar Yahaya ya bada tabbacin cewa lallai a karkashe jagorancin sa sojoji za su maida hankali wajen ganin an gama da Boko Haram, al’amura sun koma yadda suke.