Ƙungiyoyin ‘yan ta’adda biyu, Boko Haram da ISWAP sun haɗe wuri ɗaya, a ƙarƙashin amincewa da shugabancin AlƘuraishi.
Makonni kaɗan da Shekau ya yi mutuwar ɗanyen-kasko, lokacin wata sa-in-sa ɗin sa da shugabannin ISWAP waɗanda su ka ƙure masa gudu, a yanzu ta tabbata cewa Boko Haram da ISWAP sun haɗe wuri ɗaya, su ka sun sasanta saɓanin da ke a tsakanin su.
A wani bidiyo na minti 13, an nuno dakarun ɓangarorin biyu su na ɗara hannayen su akan hannayen junan su.
A lokaci ɗaya kuma an nuno su na rera waƙar mubayi’a, miƙa wuya da haɗewar danƙon zumuncin da ke tsakanin su.
Hadewar dai ta na nufin a yanzu duk sun miƙa wuya sun yi mubayi’a ga Aba Ibrahim Al-Hashimiyil AlKhuraishi, wanda su ka sa wa sunan -Khalifan Musulmai’.
A bidiyon dai an nuno mayaƙa hudu daga ɓangaren Boko Haram da ISWAP su na yin mubayi’a ga sabon ‘Khalifan na su a cikin yaren Hausa, Turanci, Larabci da Fulfulde.
Wani daga cikin mai magana a cikin su, ya yi iƙirarin cewa tun can farko jami’an leƙe asiri ne su ka raba kawunan su.
“A baya abokan gabar mu sun yi galabar raba kawunan mu. Amma yanzu mun haɗe wuri ɗaya.
PR Nigeria ta ruwaito cewa babban jami’in soja Abdulrahman Ƙuliya, wanda ya mutu a hatsarin jirgin saman sojoji tare da Janar Ibrahim Attahiru, shi ne ya yi ƙoƙarin da ya yi har ya raba kawunan Boko Haram da ISWAP.
Wannan saɓani dai ya yi sanadiyyar mutuwar Shekau.
A bidiyon dai na baya-bayan nan, Boko Haram ne su ka fara yin jawabin tare da yin mubayi’a ga AlKhuraishi, tare da gode masa
“Duk wani ɗan Boko Haram da ISWAP zai ji daɗin wannan rana, domin ɓangarorin biyu sun haɗe wuri ɗaya.”
Wani ɗan Boko Haram da ya yi jawabi da Hausa, ya tabbatar wa AlKhuraishi cewa ba za su taɓa bijire wa dokar da zai shimfiɗa masu ba.
“Yanzu mun haɗe kawai. Abin da ya rage masa yanzu tashi tsaye mu yaƙi kafirai. Duk wani kafiri ya shiga uku.” Haka wani ɗan ɓangaren ISWAP ya bayyana a lokacin da ya ke bayani.
Discussion about this post