BAWA YA ZAGE DAMTSE YA ƊAUKI GORA: EFCC za ta gurfanar da ɓarayin gwamnati da ƴan ‘yahoo-yahoo’ har 800

0

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya bayyana cewa EFCC ta kammala shirin gurfanar da mutum 800 kotu nan ba da daɗewa ba.

Bawa ya yi wannan bayani ne ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, a ranar Alhamis.

Ya ce waɗanda za a gurfanar ɗin akasarin su waɗanda ake zargi da satar kuɗin gwamnati ne da riƙaƙƙun ‘yan dandatsa da damfara ta dabarun intanet, wato ‘yan yahoo.yahoo.

Ya ce an samu jinkiri ne har adadin ya taru zuwa mutum 800, saboda matsalar yajin aiki da aka fuskanta a ɓangaren ma’aikatan kotuna.

Bawa ya kuma sha alwashin cewa zai sake gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Abia, Uzor Kalu, wanda Kotun Ƙi ta sallame shi daga kurkuku bayan ya shafe watanni shida a tsare.

Kotun Ƙoli ta sallami Kalu ne daga hukuncin daga ɗaurin shekaru bakwai da aka yi masa, bayan samun sa da laifin karkatar da Naira biliyan 27.

An sallame shi ne bayan matsalar da aka samu a shari’ar, inda alƙalin da ya ɗaure shi ya yanke hukunci ne bayan an rigaya an ƙara masa girma daga Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, zuwa Mai Shari’a na Kotun Daukaka Ƙara ta Tarayya.

Haka kuma Bawa ya bayyana nasarar yanke wa tsohon Shugaban Bank PHB hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a kurkuku, bayan an kama shi da laifin satar naira biliyan 27 daga bankin.

An gurfanar da Francis Atuche kotu tun cikin 2009. Amma sai a ranar Laraba ɗin da ta wuce ce kotu ta yanke masa hukumcin.

Share.

game da Author