Hukumar Sojojin Najeriya ta bada sanarwar yadda sojoji su ka daƙile yunƙurin kai wa Sansanin Sojoji na garin Kumshe mummunan harin ƙunar-baƙin-wake.
Kumshe gari ne a jihar Barno, inda aka jibge sojoji a garin, amma Boko Haram su ka yi ƙoƙarin yi wa sojojin shigar-kutsen kai masu hari.
Kakakin Yaɗa Labarai na Sojojin Najeriya, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar da sanarwar cewa a ranar Lahadi sojojin sun fatattaki ‘yan Boko Haram waɗanda su ka je a kan motocin ɗaukar mahara masu harba manyan bindigogi da kuma wasu a kan babura.
Nwachukwu ya ce an kashe mahara shida an kuma kwace muggan makamai a hannun su.
Lamarin ya faru makonni kaɗan da sojoji su ka kashe fiye da ‘yan ta’adda 50.
Baya ga kisan Boko Haram su shida, an kuma ƙwace bindigogi shida ƙirar AK 47, muggan ƙwayoyi da kayayyakin kula da majiyyaci a hannun su.
“Sojojin Haɗin Guiwa na ‘Operation HADIN KAI da ke bataliya ta 152 da ke Kumshe sun daƙile wani harin Boko Haram da su ka nemi kutsawa sansani sojoji da kuma garin Kumshe, har an kashe mahara shida an kuma ƙwace muggan makamai da muggan kwayoyi duk a hannun su.”
Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da nuna kishi da zaƙaƙaƙuranci wajen daƙile ta’addanci a ƙasar nan baki ɗaya.
A ziyarar da Shugaba Buhari ya kai Barno cikin makon jiya, ya bayyana cewa, “za mu da sauran hutu har sai na ga zaman lafiya ya wanzu, ‘yan gudun hijira sun koma gida.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara jaddada cewa babu sauran hutu a gare su, har sai ya ga cewa an wanzar da zaman lafiya kuma dukkan masu zama a sansanonin gudun hijira kowa ya koma gidan sa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan alwashin a ziyarar da ya kai Maiduguri, babban birnin Jihar Barno a ranar Alhamis.
Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Yayin ziyarar da Buhari ya kai, ya duba yanayin yadda hukumar sojoji ke gudanar da aikin tsaro, sannan kuma ya jinjina wa Gwamna Babagana Zulum, dangane da irin ci gaban da ya samar wa jihar Borno.
Daga nan kuma ya buɗe ayyuka bakwai daga cikin sama da 500 ɗin da Gwamnatin jihar ta ce ta kammala.
“Babu sauran hutu a gare mu har sai bayan mun samar da tsaro, sannan kuma dukkan masu gudun hijira duk sun koma gidajen su.
“Ba zan taɓa mantawa ba a rayuwa ta cewa Jihar Barno ce aka fi ba ni ƙuri’u mafi yawa har kashi 90 bisa 100 na ƙuri’un da aka jefa na zaɓen shugaban ƙasa a jihar.
“Abin da aƙalla zan ci gaba da yi maku shi ne na tabbatar na maido maku da zaman lafiya a Arewa maso Gabas da sauran yankunan ƙasar nan baki ɗaya.”
“Ina cike da matuƙar farin cikin kasancewa tare da ku a wannan ziyara da na kawo, saboda ni tuni na maida Maiduguri da jihar Barno tamkar gida. Domin a nan na yi gwamna a Jihar Barno shekaru 46 baya.
“Sai dai kuma rashin jin daɗin da na ke yi, na so a ce wannan ziyara na kawo ta ne a yanzu a lokacin zan so ana cikin zaman lafiya ne na zo.”
Buhari ya nuna cewa irin hare-haren da ‘yan ta’adda su ka riƙa kaiwa kwanan baya, sun nuna har yanzu akwai sauran rina a kaba.
“To dalili kenan na kawo wannan ziyara domin na ƙarfafa ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya nan ba da daɗewa ba wanann yanki.
Buhari ya ce dukkan manyan Hafsoshi Sojojin da ya naɗa kwanan nan gogaggu ne, kuma duk sun jagoranci wani ɓangare ko ɓangarori na yaƙi da ta’addanci a baya.