Ban taɓa nuna rashin goyon bayan yi wa Kundin Dokoki kwaskwarima ba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ba ta taɓa nuna rashin goyon bayan yi wa kudin tsarin mulki kwaskwarima ba. Amma dai abin da ya ke ƙara jaddadawa shi ne, duk abin da za a nema, to a nemi biyan buƙatar a bisa tsarin da doka ta gindaya.

Buhari ya yi wannan jawabi a ranar Asabar, a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya kan Ranar Dimokuraɗiyya.

Ya ce Majalisar Tarayya ce ke da alhaki da nauyin yi wa dokokin mulki kwaskwarima.

Buhari ya ƙara da cewa gwamnatin sa a shirye ta ke wajen taimakawa a yi wa dokoki kwaskwarima, amma ba tare da ta shiga gona ko ta yi babakere a kan ayyukan Majalisar Tarayya ba.

“Yayin da wannan gwamnatin ba ta nuna rashin amincewa da kwaskwsrimar kundin tsarin mulki ba, ta yarda a nemi yin kwaskwsrimar kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Kuma haƙƙin Majalisar Tarayya ne yi wa kundin mulki kwaskwarima.”

Kwanan baya PREMIUM TIMES ta buga tsauraran matakan da ake bi wajen yi wa kundin mulki kwaskwarima.

Tsauraran Matakai 15 Da Ake Bi Kafin A Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima.

1. Da farko dai wani wani ne daga bangaren Gwamnati ko bangaren Majalisar Tarayya ko ta Dattawa, zai gabatar da ƙudirin buƙatar yin kwaskwarimar.

2. Wannan Ƙudirin Ɗaiɗaikun Mutane zai iya kasancewa daga Mamba na Majalisar Tarayya, Majalisar Dattawa ko kuma wata ƙungiya. Amma idan daga wata ƙungiya ko gungun jama’a ne, to ya kasance ya biyo ta hannun ‘yan majalisa.

3. Zai kasance Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya kowace ta kafa na ta Kwamitin Kwaskwarimar Dokokin Tsarin Mulki daban. Za su riƙa karbar bayanai muradu da ƙorafe-ƙorafe daga jama’a a zaman sauraren da kwamitocin ke shiryawa, kamar dai abin da ke kan faruwa a yanzi.

4. Daga nan kuma za a yi zabe a Majalisar Tarayya da Majalisar Dokoki.

6. Kowane ƙudirin neman yi wa doka kwaskwarima zai iya tsallake shingen amincewa ne kawai idan kashi (2/3) biyu bisa uku na mambobin Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa sun amince da ƙudirin ta hanyar zabe.

7. Kashi 2 bisa 3 na nufin 240 daga cikin 360 na mambobin Majalisar Tarayya su amince. Sai kuma 72 daga cikin Saantoci 109 su amince tukunna.

8. Da zarar an kammala zabe a Majalisar Dattawa, sai a miƙa sakamakon zabe ga Majalisar Tarayya domin tabbatarwa. Haka su ma Majalisar Tarayya za su aika wa Majalisar Dattawa domin tabbatarwa.

9. Da Majalisun biyu sun kammala amjncewa da ƙudirorin sai a tura ofishin Magatakardar Majalisa, wanda shi kuma zai tura wa Majalisun Dokokin Jihohi na Najeriya gaba ɗayan su na jihohi 36.

10. Su kuma za a bukaci kashi 2 bisa 3 na Majalisun Dokokin Jihohi 36, wato aƙalla jihohi 24 kenan su amince da kowane ƙudiri.

11. Da zarar an samu nasarar waɗannan adadi, to kwaskwarimar dokoki ta tabbata kenan. Sai kuma a kinkimo ƙudirorin daga jihohi a maido su Majalisar Tarayya da Dattawa.

12. Duk wani ƙudirin da bai samu amincewar Majalisun Jihohi aƙalla 24 cikin 36 ba, to an yi fatali da shi a kwandon shara kenan. Sai a jira can gaba bayan wasu shekaru idan an sake tayar da batun yi wa dokoki kwaskwarima.

13. Abu na ƙarshe kuma shi ne Amincewar Shugaban Kasa.

14. Da zarar Majalisun Jihohi sun maida ƙudirori a Majalisun Tarayya da Dattawa, to babu sauran bata lokaci, sai a kinkima a kai wa Shugaban Ƙasa, domin ya Rattaba Hannun Amincewa.

14. Shugaban Ƙasa zai iya sa hannu kan ƙudirin da ya ga dama. Da zarar ya sa hannu, shikenan ƙudiri ya tabbata doka cikakkiya.

15. Shugaban Kasa zai iya ƙin sa hannu kan ƙudirin da ya ga damar ƙin sa wa hannu.

Share.

game da Author