Ban ɗauki nauyin harin da aka kai garin Igangan, inda aka kore ni ba -Sarkin Fulanin Igangan

0

Sarkin Fulanin Igangan da aka fatattaka daga dajin garin wanda ke Jihar Oyo, Salihu Abdulkadir, ya nesanta kan sa daga goyon baya ko daukar nauyin wani harin da aka kashe mutane a Igangan kwanan nan.

Abdulkadir wanda aka kora daga Igangan bayan an kona masa gida da ilahirin dukiyar sa, kuma an kashe masa da, ya musanta wannan zargin ne daga Ilorin, Jihar Kwara, a ranar Alhamis.

Ya kuma yi zargin cewa mambobin OPC sun kai wa Fulani harin ramuwar-gayya har sun kashe mutum takwas a Ingangan da Elekokan kusa da Ingangan a cikin makon nan.

Amma kuma ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Oyo da kuma Gwamnatin Tarayya su yi kwakkwaran bincike domin gano masu fitinar tare da hukunta su.

“Ina so na sanar wa duniya cewa ni ko iyali na babu wanda ke da hannu a harin kisan da aka yi a Igangan.

“Tun da aka fara rikicin watanni hudu da su ka gabata, Ni da iyali na mun yi hijira mun bar Igangan. Ba a kashe yara na ko daya a wannan rikici na bayan nan ko daya ba, saboda ko daya babu wanda ke zaune a can yanzu.

“Yan OPC sun kashe Fulani takwas a Igangan da Elekokan cikin makon nan. Kuma munanan kalaman da Fatai Oeoseni, Mashawarcin Gwamnan Oyo Kan Harkokin Tsaro ya yi, ya nuna gwamnati na goyon bayan Sunday Igboho.

“Mu na kuma da rahoton yadda ‘yan iska ke tare motocin haya a Igangan su na kashe duk Bafulatanin da su ka gani a cikin motar.”

Idan ba a manta ba, a Igangan ne Sunday Igboho ya fara kaddamar da kai hare-haren korar Fulani, inda bayan kisa, aka banka wa gidan Sarkin Fulanin Igangan wuta aka kona dukiyar sa.

Sarkin Fulani Salihu ya kwashe iyalin sa ya koma Jihar Kwara.

Shi kuma Sunday Igboho ya ci gaba da ta’addancin sa, har yau ‘yan sanda ba su kama shi ba.

Share.

game da Author