Babu hujjar wai Ezekwesili ta ce garkuwar da aka yi da ‘yan matan Chibok makarkashiya ce ta ture gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan – Bincike DUBAWA

0

Ranar 14 ga watan Afrilun 2014 aka yi garkuwa da ‘yan mata ‘yan makarantar Government Girls Secondary School Chibok, da ke jihar Borno, Bayan haka, kungiyar Bring Back Our Girls (BBOG) ta bulla, a karkashin jagorancin Oby Ezekwesili, inda kungiyar ta bukaci da a sako ‘yan matan.

Ranar asabar 15 ga watan Mayu 2021 wani mai amfani da shafin Facebook mai suna @Katch Ononuju ya wallafa wani labari yana zargin cewa Madam Oby Ezekwesili ta ce garkuwar da aka yi da ‘yan matan Chibok makarkashiya ce domin ta bata sunan shugaban kasar wancan lokacin wato Goodluck Jonathan.

Har wa yau, labarin da @Katch Okokuju ya wallafa ya yi zargin cewa a wancan lokacin shugabanni filani, wadanda suke neman ganin an cire Jonathan daga karagar mulki an dora Muhammadu Buhari, sun tura hajiya Hadiza Bala, wato shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriyar (NPA) da aka dakatar, zuwa kungiyar ta BBOG.

A ranar laraba 19 ga watan Mayu 2021, wato kwanaki hudu da wallafa wannan batun, har mutane 35 sun nuna alaman ma’amala da labarin sanan akwai sharhi 39 a karkashi kuma har an tura shi ga jama’a sau 64.

Ga dai furucin da Oby Ezekwesilin ta yi a cewar Ononuju:

“Ku yi hattara idan kuna aiki da bafilatani domin a ko yaushe aniyarsu daban ta ke da abin da kake zato. Na yi aiki da Hadiza Bala Usman a shekara ta 2014 a shirin BBOG. A lokacin, ban san cewa shugabanni filani ne suka turo ta shirin domin ta lalata sunan Goodluck Jonathan domin Muhammadu Buhari ya ci zabe ba. Yanzu na yarda cewa lallai garkuwar da aka yi da ‘yan matan Chibok makarkashiya ce aka yi dan a bata sunan Goodluck Jonathan saboda Muhammadu Buhari ya yi nasara a zabe.”

An kuma sake wallafa wannan zargin a shafin kudu maso gabashin Najeriya inda ranar laraba 19 ga watan Mayu kawai, ya samu yaduwa har sau 497 kuma mutane 628 suka yi ma’amala da labarin.

To amma gaskiya ne Ezekwesili ta fadi hakan?

Tantancewa
Dubawa ta fara bincikenta a Facebook, inda ta tafi shafin Madam Ezekwesili ta gano cewa ita kanta ta yi tsokaci kan wannan zargin. Ezekwesili ta wallafa wani labarin da aka yi dangane da batun a jaridar The Cable kuma ta yi amfani da labarin ta karyata zargin tana cewa:

“Wadanda suka yada labarin karya suna jin dadi, yanzu dai murnansu ta koma ciki domin na fitar da sanarwar da ta karyata zargin. A gani na babu matsala idan mutun ya tsani Ezekwesili da dabi’unta amma ku sani cewa ba zaku taba iya karya a kai na ba. Bana karya, abin da na fada shi nake aikatawa.”

……… Rubutun da Ezekwesili ta yi wa sanarwar da ta wallafa a shafinta tare labarin jaridar Cable

Mun kuma gano wani labarin da ta wallafa kafin ta mayar da martani ga wannan zargin, a wata sanarwar da ta yi. Ezekwesili ta sanya hotunan sanarwar da ta yi wa manema labarai ta bakin kakakinta Ozioma Ubabuko, wanda aka wallafa ranar 17 ga watan Mayu 2021. Sanarwar ta kwatanta batun a matsayin sharrin makiya wadanda suke so su yaudari jama’a.

“Na tsawon shekaru bakwai yanzu, mutane ke yada karairayi da jita-jita a kai na saboda na zabi in yi rayuwa bisa turbar gaskiya a kasar da ke yabwa karya. Saboda ina sadaukar da kai na in dauki nauyin abubuwa ko da kuwa sun kasance a yanayi mai tsaurin gaske, a lokutan da saura sukan kawar da kai. Ba kuwa za su taba yin nasara ba saboda na iya shawo kan matsaloli. Ina matukar godiya da irin halin da nake da shi. Haka nan kuma ba abun da zai sa ni yin nadaman kiran da na yi a shekarar 2014, na ceto ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok su 219 wadanda ba su ji ba su gani ba.”

Ezekwsili ta kuma sake wallafa batun a shafinta na Twitter.

DUBAWA ta sake duka shafukan da Ezekwesili ke da su a yanar gizo dan ganin ko za ta wani abu dangane da ‘yan matan Chibok daga 15 ga watan Mayu zuwa yanzu amma ba ta ga komai ba.

A Karshe

Daga binciken DUBAWA, sanarwar manema labaran da Madam Ezekwesili ta bayar da kuma duk abubuwan da ta wallafa a shafukanta na yanar gizo, babu wani abin da ya nuna cewa ta yi wannan furuci. Dan haka babu wata hujja da ta tabbatar da sahihancin wanann zargi.

Share.

game da Author