Ba mu son ganin ko Bafulatani ɗaya tal a yankin Yarabawa daga ranar litinin – Sunday Igboho

0

Tantagaryar ɗan iskan yankin Yarabawa, mai ɗaukar doka a hannun sa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bai wa dukkan Fulani makiyaya mazauna jihohin Yarabawa wa’adin daga ranar Litinin mai zuwa ba ya son ganin ko Bafulatani makiyayi ɗaya tal a jihohin yankin.

Wannan sabon gargaɗi ya fito ne a wata tattauna da Kakakin Yaɗa Labaran sa, Oluyomi Koki ya yi da shi kuma ya watsa ga manema labarai a ranar Laraba.

“Mu na sanar da cewa daga ranar Lininin mai zuwa, ba mu son ganin ko da Bafulatani makiyayi ɗaya tal a cikin jihohin Ekiti, Lagos, Oyo, Ogun, Ondo da Osun.

“Kuma daga nan ni ma zan riƙa fita mu na fatattakar duk wanda ya ƙi ficewa.

“Daga ranar Litinin kada mu ƙara jin labarin an yi garkuwa da wani Bayarabe ko ɗaya.

“Zan karaɗe dukkan dazukan jihohin Yarabawa domin na tabbatar babu wani makiyayi Bafulatani da ya ragu cikin dazukan waɗannan jihohi.”

Igboho dai ya ce bai yiwuwa a ce wasu tsirarun ƙabila ba su wuce su miliyan shida ba, amma su addabi mutum kusan miliyan 250.

Har yau dai jami’an ‘yan sanda ba su kama Sunday Igboho ba.

Share.

game da Author