APC za ta tattara komatsan ta, ta yi gaba tare da Buhari cikin 2023 -Inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa APC mai mulki ba za ta yi ƙarkon da za ta ƙara mulkin Najeriya ba, bayan saukar Shugaba Buhari a 2023.

PDP ta ce wannan wani ƙudiri ne da ƴan Najeriya su ka sha alwashin tabbatarwa, domin sun gane matsawar APC na kan mulki, to babu sauran zaman lafiya, tsaro, haɗin kan jama’ar Najeriya da kuma bunƙasar tattalin arziki a ƙasar nan bayan 2023.

Wannan bayani na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar ga manema labarai a yau Litinin a Abuja.

Kakakin ya ƙara da cewa duk wani sagarabtu da bankaurar da Shugaba Buhari ke yi don ganin ya sake ɗora APC kan mulki a Najeriya, tuni ya makara, domin ‘yan Najeriya sun gaji da mulkin maƙetaci, masu wawure dukiyar ƙasa da kuma haifar da maɓarnatan ‘yan bindigar da kisa da zubar da jini ya zame wa jiki, waɗanda su ka hargitsa ƙasar nan cikin shekaru shida.

Kola Ologbondiyan ya ce PDP na sane kuma kar ta ke kallon yadda wasu ‘yan nanaye ke ta ƙoƙarin zaburar da Buhari ya fara yi wa APC kamfen tun yanzu.

Ya ce APC ba za ta taɓa ƙalla wa ƙasar nan alheri ba, domin jam’iyya ce da aka kafa bisa doron bi-ta-da-ƙulli, ƙarairayi, alƙawurran ƙarya, wuru-,wurun zaɓe, goyon bayan kashe-kashe, sata, wariyar yanki da ɓangarenci da kuma tantagaryar nuna ƙiyayya.

Don haka ta ce APC ba za ta iya ceto Najeriya bayan Buhari ya kammala wa’adin sa cikin 2023 ba.

Share.

game da Author