Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa Uche Secondus, ya bayyana cewa jam’iyar APC ta yi shirin shirya maguɗin zaɓen shugabancin ƙasar nan a 2023 ta hanyar yin amfani da gwamnonin APC baki ɗayan su da ke mulki.
Secondus ya yi wannan iƙirari a ranar Talata, ranar da Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya koma APC daga PDP.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a Abuja, Secondus ya ce jama’a sun gaji da APC na mulkin Najeriya, shi ya sa jam’iyyar za ta yi amfani da ƙarfin gwamnonin jam’iyyar na faɗin ƙasar nan domin su shirya maguɗi a zaɓen 2023.
Sai dai kuma ya ce PDP za ta bi dukkan hanyoyin da su ka dace domin ganin ta kayar da APC a zaɓen na Shugaban Ƙasa mai zuwa.
Da ya ke magana kan Matawalle, Secondus ya ce Matawalle da sauran gwamnonin Cross River da Ebonyi, waɗanda su ka koma APC, maciya amana ne.
Ya ce PDP za ta bi ƙa’idar kotu domin ƙwato kujerar gwamnan Zamfara daga hannun Matawalle a APC.
“Dama Kotun Ƙoli ce ta bai wa PDP bayan an haramta wa APC mulkin Zamfara. Tunda ya koma APC, za mu koma a karɓo mana kujerar mu. Idan ya ga dama sai ya koma ziƙau shi kaɗai.” Inji Secondus.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da PDP ta ce idan ka koma APC za mu ƙwace kujerar gwamna a hannun ka.
Jam’iyyar PDP ta gargaɗi Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara cewa idan ya koma APC zai rasa kujerar sa ta gwamna sukutum.
A cikin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, Kakakin Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya jaddada wa Matawalle cewa PDP ta ci zaɓen Gwamnan Zamfara ne da ƙuri’u, kuma Kotun Ƙoli ce ta tabbatar masa da kujerar.
Saboda haka ya ce tunda INEC ta haramta wa APC muƙaman gwamna, na mataimaki, sanatoci da na ‘yan majalisar tarayya, kuma Kotun Koli ta tabbatar, don haka doka ta haramta wa APC yin mulki a jihar Zamfara kenan, tsakanin 2019 zuwa 2023.
Haka kuma PDP ta gargaɗi ‘yan Majalisar Dattawa da na Tarayya na Jihar Zamfara har ma da na Majalisar Dokoki na jiha cewa kada su bari a ribbace su har su rasa kujerun su.
“Saboda dokar ƙasa dai ta ce ‘yan majalisa ba za su canja sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan ba, har sai idan akwai rikici na cikin gida a cikin jam’iyyar su.
“Kasassaɓar da Bello Matawalle ke son yi ganganci ne ƙarara, domin zai burma wa cikin sa wuƙa ne kawai. Saboda dokar INEC da kuma Kotun Koli duk sun haramta wa APC yin mulki a jihar Zamfara, saboda kwata-kwata ba su cikin ‘yan takara.”
APC dai ba ta cikin jam’iyyun takara a Zamfara, saboda ta
ba a yi zaɓen fidda-gwani bisa ƙa’ida ba. A kan haka ne INEC da Kotun Koli su ka hana su takara.
Yanzu dai Matawalle ya koma APC, kuma a wurin karɓar sa a ranar Talata a Gusau, an riƙa jin miryoyin mutane na cewa “ba ma so.”