Sai da aka shafe shekaru har biyu da wata shida, sati daya da kwana biyu ana gwabza yaki tsakanin jami’an tsaron kasar Najeriya da musanman sojoji da kuma yan aware na kabilar inyamurai masu fafutukar neman yancin kasar kabilar igbo kamar yadda suke kiran kansu a zahiri, yakin wanda sojan nan mai rike da mukamin canal a gidan soja Odimegwu ojukwu ya jagoranta daga ranar 6 ga watan yuli na shekarar 1967 xuwa 15 ga watan janairu na shekarar 1970 ya jawo hasarar rayuka da tarin dukiyoyi masu yawa.
Odimegwu Ojukwu wanda ya kalubalancin shugabanni daga yankin arewacin Najeriya da cewar sune suka kwashe kaso mai yawa daga albarkatun kasa tare da rike duka wasu manyan mukamai a gwamnatin tarayya, sannan ya kara hura wutar gaba da kiyayya a tsakanin kabilar inyamurai da kuma sauran kabilun Najeriya musanman ma na arewa.
Rahotanni a wancan lokacin sun tabbatar da mutuwar sama da mutun miliyan daya tare da tursasa wasu gudun hijira zuwa makotan kasar nigeria da wasu sassa daban na fadin duniya, inda mata suka zama zawarawa, yara suka zama marayu, baya ga masifar yunwa da bakin talauci da yayi kaka gida musanman ma a yankin na kabilar inyamurai.
Tarihi ya tabbatar da cewar matasa sune ke dauke da kaso mai yawa na adadin rayukan da inyamurai suka rasa a lokacin juyin juya halin da sunan yakin neman yanci wanda hakan ya zama hasara babba ga mazauna wannan yankin.
Abunda yafi bada mamaki shine yadda matasa a wannan yankin yanzu suka yi watsi da littatafan tarihi, masana a yankin suka kasa wa’azantar da matasan na yanzu sannan kuma manyan su suke cigaba da dauke kai daga abunda ke faruwa wanda idan ba sa’a ba tarihi zai maimaita kansa kuma barnar yanzu sai ta linka ta baya idan akayi la’akari da cigaba da kimiya da ilimi na kirkira yazo da su a daidai wannan lokacin.
Marigayi tsohon shugaban kasar kudancin Afrika Nelson Mandela bayan ya gama cin sarka a gidan kaso haka ya sake dawowa yana cigaba da rajin kare bakar fata a kasarsa batare da ya dau makami ba kuma baiyi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa na azo agani ba har ya kaiga cin nasara a fafutukar tasa karshe yau duka duniya na girmamasho saboda irin waccan gudunmawa daya bayar a kasar tare da sauya tsarin mulkin kasar, tabbas wannan ya sha banban da tsatsarin da shugaban masu neman yancin inyamurai na baya odimegwu ojukwu da na yanxu Nmadi Kanu suke bi, wanda na yanzu ko zaman kasar ma ba yayi, Sai dai kwangilar rusa zaman lafiya na yankin nasu da kuma zuga matasa kauracewa hadin kai domin cigaban Najeriya.
Tabbas jahilci cuta ce babba dake rusa tunani tare da jefa mutun cikin kunci na halin kaka nikayi da rashin kwanciyar hankali wanda hakan yasa suka kasa yin tunani nagari domin rayuwarsu ta inganta duk kuwa da tarin masana da suke dasu a yankin nasu.
Adamu Saleh maidalibai kazaure
Dalibi a jami’ar Bayero dake cikin Birnin Kano
Discussion about this post