Ana ƙoƙarin kafa dokar bai wa matasa kashi 40% bisa 100% na kujerun Majalisa -Sanata Omo-Agege

0

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa Majalisar Dattawa na nan ta na aiki gagarimi a kan wani ƙudiri, wanda idan ya zama doka, zai bayar da kashi 30 bisa 100 na kujerun Majalisar Tarayya ga matasa.

Haka kuma ya ce ƙudirin dokar zai bai wa matasa kashi 40 bisa 100 na kujerun Majalisar Dokokin faɗin jihohin ƙasar nan.

Omo-Agege ya yi wannan bayani a Lokoja babban birnin Jihar Kogi, a ranar Juma’a, wurin taron murnar cikar Gwamna Yahaya Bello shekaru 46 a duniya.

Take takardar da Omo-Agege ya gabatar dai shi ne “Matsalar Tsaro a Najeriya da Kuma Rawar da Matasa ke takawa.”

“Idan har aka bai wa matasa waɗannan gurabu masu yawa a Majalisun Tarayya da na Jihohi, to za a wayi gari matasa ba su ma da lokacin fitowa su yi zanga-zanga, domin su na can sun maida hankali wajen zaman majalisa.”

Sanata Ovie Omo-Agege dai shi ne Shugaban Kwamitin Yi Wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da ake amfani da shi kwaskwarima.

Masu ƙorafe-ƙorafe na ganin cewa kundin an shirya shi ne a lokacin da sojoji ke gaggawar miƙa mulki ga farar hula cikin 1999.

Ya ƙara da cewa da zarar an samu ƙarin matasa a majalisu na jihohi da na tarayya, to matasa za su maida hankali wajen harkokin gaban su, su daina maida hankula wajen aikata laifuka.”

Agege ya jinjina wa Yahaya Bello a matsayin sa na gwamna mafi ƙanƙantar shekaru a cikin gwamnonin Najeriya 36.

Kuma ya ce ita kan ta jam’iyyar APC na alfahari da Gwamna Yahaya Bello bisa ayyukan raya ƙasa masu ɗimbin yawa da APC ta ce gwamnan ya aiwatar a Jihar Kogi.

Share.

game da Author