Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa mahara sun yi garkuwa da mutum 12 a wani kauye dake mahadar titin Awon zuwa Mothercat dake karamar hukumar Kachia.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Mohammed Jalige ya sanar da haka ranar Alhamis a Kaduna.
Jalige ya ce maharan sun far wa kauyen ranar Laraba da misalin karfe tara da minti ashirin na dare suna harbi ta ko ina.
“Maharan sun yi awan gaba da mutum 12 amma jami’an tsaro sun ceto mutum biyu daga cikinsu.
Bayan haka Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan wanda ya yi jawabi a madadin gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i ya yi kira ga mutane da su rika bada bayanan sirri domin taimakawa jami’an tsaro wajen samun bayanai game da ayyukan mahara.
Yayi wannan jawabi ne a ziyara ta musamman da tawagar gwamnati da jami’an tsaro suka kai wannan karamar hukuma.
Jihar Kaduna kaman sauran jihohin yankin Arewacin kasar nan ta yi kaurin suna wajen fama da matsalar rashin tsaro.
Aruwan ya gana da mutanen garin sannan ya mika sakon jaje ga mutanen garin daga gwamna El-Rufai.