An kashe mutum ɗaya, an ƙona gidaje 50 tsakanin ƙabilun Shongom da Filiya a Gombe

0

Aƙalla mutum ɗaya aka kashe, sannan aka ƙona gidaje sama da 50 a wani mummunan rikicin gona da ya barke tsakanin ƙabilun yankin gundumar Shongom da na Filiya, a Jihar Gombe.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya ne ya bayyana haka bayan fitowa daga taron Majalisar Tsaro ta Jihar Gombe.

Ya ce rikicin ya barke ne tun a ranar Asabar, inda aka kashe wata mata ɗaya kuma aka banka wa gidajen a kimanin 50 wuta.

An ɗibga asarar kayan abinci, kayan masarufi da sauran kayyyakin amfani na yau da kullum.

Ya ce Gwamnatin Jihar Gombe ta yi tir da tashin hankalin, kuma ta gargaɗi al’ummobin bangarorin biyu su rungumi zaman lafiya da juna.

“Sannan kuma Gwamnatin Jihar Gombe ta umarci Mai Kaltungo, Sale Mohammed ya shiga tsakani domin a sasanta kuma raba rikicin tare da shiga tsakani.

“Majalisar Tsaron Jihar Gombe na ƙara jaddada cewa har yanzu dokar haramta ƙungiyoyin banga da na farauta na nan ba a cire ta ba. Kuma an umarci jami’an tsaro su yi maganin waɗanda su ka karya wannan dokar.” Inji shi.

Ya ƙara da cewa an umarci shugabannin bangarorin ƙabilun biyu su zauna da matasan yankunan su domin a tabbatar da an kauce wa sake afkuwa da kuma ƙara bazuwar rikicin a wasu yankuna.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Gombe, Adamu Dishi, ya ce tuni zaman lafiya ya dawo a yankunan.

“An kuma umarci jami’an tsaro su zaƙulo tare da damƙe duk wani mai hannu a barkewar rikicin, domin a hukunta shi.”

Share.

game da Author