An kama shugaban makarantar da saura kiris ya yi lalata da ɗalibar sa ƴar shekara 14 da karfin tsiya

0

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama shugaban makarantar sakandare ‘Megland Comprehensive’ dake Lekki Emmanuel Madueke mai shekaru 62 da laifin kokarin yi wa ‘yar shekara 14 fyade.

Hukumar kare hakin yara da matan da aka ci zarafin su na jihar Legas (DSVRT) ta sanar da haka ranar Lahadi.

Hukumar DSVRT ta sanar da haka ne bisa ga binciken da ta gudanar a makarantar bayan ta samu labarin abinda shugaban makarantar yake aikatawa da ƴay mutane a makarantar.

Sakamakon binciken ya nuna cewa yarinyar dalibace a makarantar, ya nemi ya yi lalata da ita a ranar da ake taron yara wato ranar 27 ga watan Mayu.

Kodinatan DSVRT Titilola Vivour-Adeniyi ta ce yarinyar ta bayyana musu cewa a wannan ranar Madueke ya sumbace ta sai ta falfala da gudu.

“Ta ce tun daga wannan lokaci Madueke yake kokarin ganin ya yi lalata da ita amma bai samu nasara ba.

Titilola ta ce sakamakon binciken da Suka gudanar a makarantar ya nuna cewa wannan ba shine karon farko ba da Madueke ke aikata irin haka da ƴara a makarantar ba.

“Ya kan ce musu lallai idan basu bashi hadin kai ba zasu faɗi jarabawa, idan kuma suka biya masa bukata, sun dinga cin jarabawa kenan har sai sun gama wannan makaranta.

A yanzu dai Madueke na hannun ƴan sanda sannan ita ma rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Hukumar DSVRT ta ce gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda ke cin zarafin mata da yara a jihar ba.

Share.

game da Author