Jami’an tsaro sun harbi mutum biyu cikin masu zanga zangar rashin tsaro da suka tare motar gwamnan Kebbi Atiku Bagudu.
Zanga-zangar ya biyu bayan kashe mutane 88 da ƴan bindiga suka yi a wasu kauyuka a karamar hukumar Danko-Wasagu a ranar Alhamis.
Wasu masu zanga zangar sun kone wani mota dake cikin tawagar gwamnan jami’an tsaron sunyi harbin ne domin tarwatsa masu zanga zangar.
Shaidu sun bayyanawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa mutanen da aka harba suna Asibiti suna karbar magani.
Sunce gwamna Bagudu yaje yankin ne domin jajen wadanda aka kashe a harin da yan bindiga suka kai, amma matasa sun fito sun kona tayuyi da kuma yiwa gwamnan ihu saboda tabarbarewar tsaro a yankin nasu mai makwabtaka da Jahohin Zamfara da Nija.
Sarkin Zuru, Muhammadu Sani-Sami, ya tabbatar da faruwar hakan a wata hira da yayi da BBC Hausa, sarkin ya ce gwamnan yaji yankin ne domin jajantawa al’ummar yankin.
Dama shi gwamnan mutum ne mai yawan zuwa jaje idan yanayi irin haka ya faru kuma yana alkawarin cewa hakan bazai kuma faruwa ba.
“Amma da alamu matasan sun gaji da alkawari babu chanji na samar da tsaro shi yasa suka fito suka nuna bacin ransu, inji Sarkin na Zuru.
Sai dai sarkin yace gwamnati tana iya komarinta wajen yaki da yan bindiga amma jami’an tsaron dake sunturi a yankin basu dayawa.
Akarshe gwamnan ya jajantawa mutanen yankin da abin ya faru kuma yayi alkawarin inganta tsaro a yankin.
Discussion about this post