Duk dai a cikin hirar da Buhari yayi da Talbijin din Arise, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ta kaya tsakanin aa da wasu gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma da suka zo wurin sa kawo karar Fulani Makiyaya.
” Wasu gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma sun garzayo nan kwanakin baya wai sun zo ne su kawo karar fulani makiyaya.
” Gwamnonin sun ce wai fulani na cinye musu amfanin gona kuma suna kashe masu gona. Sai na Tambayesu na ce wai shin ku ba gwamnoni bane wanda kuka yi alkawari tsakanin ku da mutanen ku a lokacin neman zabe, me ya sa ba za ku je ku yi aikin ku ba a matsayinku na gwamnoni, ku je can ku bi diddigi ku yo farautar masu laifi kuma ku hukunta su, sai kuzo min nan in yi muku me ne. Haka na fatattake su su koma jihohin su su yi aiki, ba su zauna suna jiran wani yayi musu ba.
” A matsayinka na gwamna, dole ya kasance kana tare da mutanen ka, tun daga kananan hukumomi zuwa sarakunan gargajiya wanda haka ake yi a da.
” Su dagatai da sarakuna sun sai duk wani kwaro da kangararre a yankunan su. Idan aka yi aiki da su za a iya kawo karshe wadannan matsaloli. Wannan shine gaskiyar magana.
Discussion about this post