A ranar Talata kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Filato Nimkong Ndam ya bayyana cewa mutum 441 sun kama cutar amai da gudawa kuma cutar ta yi ajalin mutum 6 a jihar.
Ndam ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Jos.
Ya ce an gano wadannan mutane ne a kananan hukumomi bakwai a jihar.
Ndam ya ce kwayoyin cutar ‘Vibrio cholera’ ke haddasa cutar amai da gudawa ko kuma cutar kwalara a jikin mutum.
Ya ce mutum na kamuwa da cutar idan akwai kwayoyin cutar a cikin ruwa ko abinci a dalilin rashin tsaftace muhalli.
A dalilin haka ya yi kira ga mutane da rika tsaftace muhallin su, su rika dafa ruwan sha da wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.
Ndam ya yi kira ga mutane da su rika hanzarin zuwa asibiti a duk lokacin da aka ga alamun cutar mai makon a zauna a gida ana ‘yan dabarun da ba zai yi magani ba, a karshe kuma a yi da na sani.
Alamun cutar amai da gudawa.
Kadan daga cikin alamomin kamuwa da cutar sun hada da Zazzabi, Amai da zawo, kasala a jiki, rashin iya cin abinci da yawan Suma.
Hanyoyin Kare kai daga kamuwa da Kwalara
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
Discussion about this post