Allurar rigakafin COVID-19 ba ta rage tsawon kwanakin rayuwa – Binciken DUBAWA

0

Zargi: A cewar wani sakon da ake yadawa a manhajan whatsapp, allurar rigakafin COVID-19 na rage tsawon rai kuma yana hana haihuwa.

Yayin da ake cigaba da yi wa jama’a allurar rigakafin COVID-19 mun ga karuwar ra’ayoyi mabanbanta, wadansun marasa gaskiya kuma masu cike da yaudara, hatta zargin cewa an kirkiro allurar rigakafin ne domin a rage yawar al’ummar duniya.

Ba da dadewa ba wani sako a manhajan whatsapp ya yi zargin cewa allurar rigakafin zai rage tsawon ran duk wanda ya karba. Ga wadanda suke kasa da shekaru 50 na haihuwa, zargin ya ce ana kiyasin za su mutu tsakanin shekaru 5 zuwa 10 daga karbar allurar rigakafin yayinda wadanda ke da shekaru sama da saba’in su kuma kwanan su zai kare cikin shekaru biyu zuwa uku daga sadda suka karbi allurar.

Sakon wanda ya danganta zargin da wata Farfesa Dolores Cahill ya kuma kara da cewa allurar ba ta tsaya nan ba, tana ma da karfin hana haihuwa ko kuma rage karfin namiji.

Ga kadan daga cikin abun da sakon ke fada ….

Ta ce duk wanda ya karbi allurar rigakafin zai mutu cikin shekaru biyar zuwa goma. Duk mai shekaru sama da saba’in, idan har ya sami allurar rigakafin zai gamu da ajalin shi cikin shekaru biyu zuwa uku. Sai dai mafi mahimmanci shi ne mutun zai rasa karfin haihuwa. Ana kiranta farfesa Dolores Cahill. Farfesar bajamushiya ce wadda ta kirkiro wani nau’i na daya daga cikin sinadarin abinci mai suna protein a turance da kuma wata dabara ta amfani da na’aura mai sarrafa kanta. Bacin haka, Cahill kwararriya ce a fanin kimiyyar nazarin halittu. Aikinta ya karkata ne ga gudanar da binciken kan nau’in na protein da yadda za’a iya amfani da shi a yanayin illimin halitta.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da tattara bayanai dangane da farfesa Cahill da kuma gudanar da bincike kan zargin.

Wace ce Dolores Cahill?

Kafin 18 ga watan Maris 2021, dokta Dolores Cahill malama ce a jami’ar Dublin wato University College of Dublin ko kuma UCD a takaice. Farfesar ta kuma kasance jagorar jam’iyyar masu kishin kasa ta Irish Freedom Party kafin ta yi murabus ranar 22 ga watan Maris 2021.
Naciyar da ta rika yi tare da yawan zargi mara tushe dangane da COVID-19 a kafafen sadarwa na yanar gizo ya sa wani kwamitin kimiyya na tarayyar Turai ya bukaci da a sauke ta daga matsayinta na koyarwa a makarantar.

To sai dai bincikenmu bai nuna mana wani abin da ya danganta Cahill da sakon da ke yawo a manhajan Whatsapp ba. Amma mun ga kadan daga cikin ire-iren zargin da ta yi a baya.

Zarge-zargen Dr. Cahill

Dr Cahill wadda farfesa ce a fannin Translational Science ko kuma kimiyyar warware matsalolin da suka danganci cututtaka a jami’ar UCD, ta kasance daya daga cikin jagororin adawa da matakin gwamnatoci na sanya takunkumin takaita zurga-zurga da ma amfani da kyallen rufe fuska wato facemask lokacin da ake fama da barkewar cutar COVID-19. Ta ma taba cewa kananan yaran da ke amfani da kyallen rufe fuska na fama da karancin iskar shaka kuma wannan zai rage kaifin kwakwalwarsu.

Haka nan kuma Cahill ta ce matakan takaita zurga-zurga ko kuma ma sanya tazarar da ake yin a mita daya da rabi tsakanin jama’a basu da amfani wajen dakile yaduwar kwayar cutar tunda duk wanda ya kamu da cutar ya warke zai sami garkuwar da za ta kare shi daga sake kamuwa da cutar har abada bayan kwanaki 10 kacal. Daga nan kuma ta ce ana iya samun kariya daga masassarar cutar da ma mutuwa idan aka sha magungunan da suka hada da Vitamin C, (wanda ake samu daga lemu da ‘ya’yan itace da ma wasu ganyayyaki) Vitamin D (wanda ake samu daga kifi, nama, kwai ko kayan ciki da kuma hasken rana) da zinc (wanda ke inganta garkuwar jiki).

Cahill ta kuma nuna adawa da allurar rigakafi inda ta yi zargin ‘yan siyasa da kafafen yada labarai na amfani da COVID-19 su firgita jama’a a wani mataki na yin farfagandar da za ta taimaka musu wajen anshe ‘yancin jama’a domin su yi ciwo dan su tilasta musu karbar allurar rigakafin.

Kasidar da ta wallafa wannan labarin ta tantance zargin na Cahill kuma ta tabbatar cewa duk bayanan karya ne, wadanda ba su da tushe kuma za su yaudari jama’a.

Lokacin da ta ke mayar da martani, Hukumar Zartarwar Turai ta ce zargin da Cahill ke yi na iya janyo lahani idan har aka dauki bayananta a matsayin zahiri.

Tsohon wurin aikinta jami’ar UCD ma ta nisanta kanta daga duk kalaman na ta.

DUBAWA ta tuntubi Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wadda ita ma ta karyata zargin Dr Cahill tunda duk alluran rigakafin COVID-19 da ake amfani da su yanzu, an riga an gwada an kuma tabbatar ba su da lahani ko ma hatsari ga kwayoyin halittar dan adam.

“Ba mu da wata hujjar wannan. Duk alluran rigakafin COVID-19 har da wadanda ake sarrafawa da kwayoyin halitta, na kare rayuwa kuma yana hana kamuwa da cutar COVID-19. Fasahar allurar rigakafin da ake sarrafawa da kwayoyin halitta na mRNA, fasaha ce da aka gwada sosai dan tabbatar da amincinta. Kuma sakamakon gwaje-gwajen da aka yi sun nuna cewa alluran na mRNA na baiwa jiki garkuwar da ke dadewa sosai. An yi shekaru gommai ana binciken fasahar allurar mRNA, hatta a cututtukan da suka hada da Zika da cutar Rabies (wanda ake samu daga cizon dabba kamar kare) da kuma mura. Allurar mRNA ba kwayoyin cuta masu rai ba ne kuma ba su da lahani ga kwayoyin halittar dan adam.” … Bayanin mai magana da yawun WHO

Batun cewa COVID-19 na hana haihuwa ko kuma karfin namiji, shi ma karya ne domin an tattauna yiwuwar haka dangane da kwayar cutar ne ba maganin ba. A rahoton wani binciken da aka yi a 2020 an gano cewa wadanda suka warke daga COVID-19 na iya samun matsalolin da suka danganci rashin sha’awar yin jima’i da kuma rashin haihuwa daga baya. Sai dai rahoton ya kara da cewa hakan ba lallai ba ne, tilas a gudanar da bincike a kuma dauki hotunan alzakarin namiji ne kadai za su iya gano ko cutar ta raunata karfin yin jima’in namiji.

Haka nan kuma rahoton ya bayar da shawarar cewa allurar rigakafi da bin dokokin kariyar da aka gindaya dan kaucewa kamuwa da cutar za su iya kare mutun daga ire-iren illolin.

Ana kuma iya duba rahoton da DUBAWA ta yi kan allurar rigakafin COVID-19 da matsalolin haihuwa a maza da mata. Rahoton ya nuna cewa allurar ba ta da lahani a wannan fannin.

Yayin da ake cigaba da gudanar da binciken kan kwayar cutar, Hukumar CDC da kungiyar likitocin haihuwa da na mata a Amirka sun ce cikin alluran da ake amfani da su yanzu, babu allurar da ke haddasa wannan matsalar.

A Karshe

Zargin da ake dangantawa da Dr. Cahill karya ne. DUBAWA ba ta ga wani wuri takamaimai inda za a ce Cahill ta yi wannan magana ba. Bacin haka binciken WHO da ma sauran cibiyoyin bincike masu nagarta ba su amince da wannan zargin ba. Ko da ma ya kasasnce Dr. Cahill ta fadi haka, sunan da ta yi wajen yada bayanai marasa tushe dangane da COVID-19 zai sanya alamar tambaya kan dacewarta ta yi irin wannan furuci sa’annan bayanan COVID-19 da suka fito daga wurinta su ma tabbas za su kasance marasa aminci.

Share.

game da Author