Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ta kafa zaratan musamman domin tabbatar da sun ceto ɗaliban Islamiyyar garin Tegina daga hannun ‘yan bindiga.
Sanarwar na cikin wata takardar da Kakakin Yaɗa Labarai ta Jihar Neja, Mary Barje ta fitar a ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar Neja.
Gwamna Abubakar Bello ne ya sanar da kafa zaratan a lokacin da yake masu jawabi yayin da aka tura su Ƙaramar Hukumar Rafi da ke cikin Jihar Neja ɗin.
An dai sace ɗaliban da ƙarfin tsiya a ranar 30 Ga Mayu, yayin da gungun ‘yan bindiga da ke kan babura su ka kutsa garin Tegina da rana tsaka, su ka sace ɗaliban.
Gwamna Bello ya ce lokacin da Gwamnatin Jihar Neja za ta fito a yi ta ta ƙare ya zo. Ya ce za a yi fitar-farin-ɗango a kakkaɓe ƴan bindiga da ke cikin dazukan jihar Neja.
“Za mu ba ku dukkan goyon bayan da ku ke buƙata domin ku aiwatar da dukkan tsare-tsaren da za su tabbatar kun ceto mana yaran nan kun dawo da su da ran su da lafiyar su. Kuma mu na fatan za ku ceto dukkan sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa daga cikin daji.
“Sun fara da fatattakar manoma daga gonakin su, su na hana su noma. Daga nan kuma su ka afka banka wa gonaki wuta.
“Daga nan kuma su ka koma garkuwa da mutane, tare da tilasta mu rufe makarantu. To kuma Allah kaɗai ya san abin da za su ɓullo da shi nan gaba.” Inji Gwamnan Neja.
Tun da farko Gwamna ya gana da iyayen yaran a Fadar Sarkin Kagara, Ahmed Gunna. Ya shaida masu cewa su ƙara juriya da dauriya, domin gwamnati na bakin ƙoƙarin ta ga an ceto masu ‘ys’yan su.
Shugaban Salihi Tanko Islamiyya inda aka saci ɗaliban Tegina, Abubakar Alhassan ya ce yanzu malaman makarantar sun yi gudun hijira zuwa sansanin sojoji a Birnin Gwari, Jihar Kaduna.
Discussion about this post