Ƴan bindiga sun kashe mutane 88 a Kebbi

0

Ƴan Sanda a Jihar Kebbi sun tabbatar da mutuwar mutane 88 sakamakon harin yan bindiga a karamar hukumar mulki ta Danko-Wasagu.

Mai magana da yawun Yan Sandar Jihar ta Kebbi, Nafiu Abubakar, ya shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa akwai fargabar yawan wadanda suka rasu zai karu saboda har yanzu ba’a ga wasu mutanen ba.

Abubakar yace ahalin yanzu ankara tura jami’an tsaro a yankin da abin ya faru mai makwabtaka da jahohin Nija da Zamfara.

Kakakin na ƴan sanda yace ƴan bindigar waɗanda ake zargi sun fito daga Jahohin Zamfara da Neja ne suka kai harin a Daren Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mazauna ƙauyukan ta ko’ina babu ƙaƙƙautawa.

Harin ya faru ne a garuruwan Koro, kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge, wadanda garuruwa ne masu wuyan zuwa saboda rashin kyawun hanyar mota, inji kakakin na yan sanda.

Yan sanda a Jihar ta Kebbi sun kirkiro sabon tsarin tsaro na ‘Operation Ganuwa’ a inda suka jibge jami’an tsaro a yankunar dake makwabtaka da Jahohin Zamfara da Nija masu fama da harin yan bindiga.

Jihar Kebbi bata da dazuka da yan bindiga suke boye zuwa suke daga makwabta shi yasa aka kirkiro Operation Gawuna domin tunkarar barayi yan bindiga, inji kakakin yan sanda Abubakar.

Share.

game da Author