Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali

0

Ƙungiya mai zaman kanta ‘Medical Women Association of Nigeria’ wace ta haɗa kawance da kungiyar ‘Advocacy in child and family health At Scale’ ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ware isassun kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali a kasar nan.

Wannan kira ya biyo bayan dakatar da tallafin Euro miliyan 3 da gwamnatin kasar Birtaniya ta ke baiwa Najeriya duk shekara.

Shugaban kungiyar Minnie Oseji ta ce janye wannan tallafi da kasar UK ta yi zai yi sanadiyyar afkawa cikin matsalolin kula da kiwon lafiyar musamman mata a kasar nan

Ta ce daga shekarar 2012 zuwa 2020 kasar Birtaniya ta tallafa wa asusun bada tazarar haihuwa ta Najeriya da euro miliyan 21 wanda aka yi amfani da su wajen ceto rayukan matan da ba za su iya hana kansu daukan ciki ba a Najeriya.

Oseji ta ce tallafin da kasar Birtaniya ke badawa duk shekara a Najeriya ya kai kashi 80% na kuɗaɗen da ake kashewa daga asusun.

Ta ce hakan ya nuna cewa Najeriya za ta cika kashi 80% na gurbin da kasar UK za ta bari a asusun.

Oseji ta yi kira ga gwamnatin UK da ta tausayawa Najeriya ta ci gaba da tallafawa fannin bada tazarar haihuwa domin ceto rayukan mata a kasar nan.

Ta kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya ta kara zage damtse wajen cika alkawarin inganta kiwon lafiya mata da yara kanana da ta yi wa kasar nan.

Share.

game da Author