Tun da nake ban taɓa ganin majalisar jihar da take a lalace, kamar majalisar jihar Kaduna a yanzu ba. Tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a kasarnan a 1999, majalisar Kaduna ke kan gaba wajen nuna bajinta a harkar majalisa.
Babu ma kamar lokacin gwamna Ahmed Makarfi. A wannan lokaci an yi jajirtattun ƴan majalisa da kan taka wa gwamna birki wanda yakan kai ga wasu ma an yi ta kai ruwa rana da su, wasu har hakan ya sa sun rasa kujerar su ta shugabancin majalisar jihar amma yanzu yadda kasan dakin asibiti shiru.
Majalisar jihar Kaduna ta zama kamar ɗakin ajiye gawa a asibiti, shiru tsit, kowa na kwance ba ka jin komai na fitowa daga majalisar, tun daga kakakin har zuwa ƴan majalisan, da ma kuma shine dalilin daya sa gwamna El-Rufai ya rungume su don ya san kwamɓar su ke. Masu tasiri a cikin su kuma aka yi kutunkutun ɗin dakatar da su.
Wasu lokuttan ma sai ka yi tambaya shin anya majalisar Kaduna na aiki kuwa ko suna hutu ne?
A irin gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna mai kurin cewa shi ɗan boko ne, ya karantu kuma da masu ilimi yake aiki ba a taɓa tunanin da kansa zai yi aiki da kakakin majalisar na yanzu ba. Amma ya yi buris saboda ya san zai iya juya shi yadda ya ke so ba tare da ya samu wani cikas ba. Da yake Aminu Shagali ya waye kuma shima ya san menene duniya ai ya kasa aiki da shi, dole aka yi kutunkutun din tsige shi a majalisar.
Babu abinda ya fi cimin tuwo a kwarya kamar yadda koda ace layi ɗaya ce ta sanarwa akan Zanga-zangar Ƙungiyar Kwadago da aka yi a Kaduna, majalisar bata ce komai ba.
Har majalisar sun je amma, ko ɗan majalisa ɗaya bai iya fitowa ya yi wa masu zanga-zanga jawabi ba koda ko karya ce zai faɗi.
Haka aka yi ta kai ruwa rana da masu zanga-zanga, ƴan jiha na fama da kansu na rashin wuta da sauransu amma zaɓaɓɓun ƴan majalisar jihar sun tafi sun ɓoye abin su.
Ya dai kamata su yi karatun ta natsu su fito su ba maraɗa kunya su yi abinda mutanen su suka aika su su yi a majalisa, su rika tunkarar fannin zartas wa da kuma kyamatar abinda bai kamata ace anyi a jihar ba.