Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Majalisar Libiya, wanda shi ne Shugaban Kasa, tare da jaddada cewa zaman lafiya ko rashin zaman lafiyar Libiya na da tasiri mai kyau ko maras kyau ga ƙasashen Yankin Sahel, ciki har da Najeriya.
“Kasashen Chadi da Nijar na da makekiyar kan iyakoki da Libiya, sannan kuma su ne makautanmu mafi kusa. To ashe kenan duk abin da ya shafi wadannan kasashe biyu, mu ma zai shafe mu. Kwanciyar hankali ko rashin sa a Libiya, zai shafe mu tabbas.” Inji Buhari.
Buhari ya kara jaddada cewa samar da tsaro a kasar nan ne babban abin da ya fi maida hankali a kai.
“Saboda idan kasa ba ta samu ingantaccen tsaro ba, babu yadda za a yi a iya kula da ita.”
Buhari ya yi murna da ganin cewa Shugaban na Majalisar Shugabannin Libiya ya halarci taron Hukumar Kula da Tafkin Chadi, wanda ya gudana a Abuja ranar Talata, domin a tattauna makomar Chadi da kuma kauce wa yadda matsalolin kasar za su iya shafar kasashen da ke makautaka da Chadi din.
A na sa jawabin, Menfi ya bayyana cewa yanzu Libiya na farfadowa a cikin hanzari, mun samu dunkulalliyar gwamnati kuma mu na kan fatattakar ‘yan bindiga da sauran sojojin haya.”
Ya ce ana kokarin farfado da tsohuwar dangantakar da ke tsakanin Libiya da Najeriya, musamman ta bangaren noma da mai. “Saboda kasashen biyu ba za su iya gudanar da harkokin su ba tare da ci gaba da kulla dangantaka da junan su ba.” Inji shi.
Buhari dai a baya ya sha nuna cewa akasarin makaman da ake ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga, duk daga Libiya ake shigo da su nan kasar, bayan kifar da gaamnatin Ghadafi.
Discussion about this post