Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani ya yi kira ga sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Farouk Yahaya ya maida hankali wajen kawo karshen hare-haren ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga.
Mai taimaka wa kakakin Jihar Kaduna kan harakar watsa labarai, Ibrahim Danfulani, ya bayyana cewa Honarabul Zailani ya hori Janar Yahaya ya yi amfani da kwarewar sa wajen dagargaza yan ta’adda da mahara da suka addabi kasar nan.
Zailani wanda shine Kakakin shugabannin majalisun dokokin jihohin Arewa Maso Yamma ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na zabin janar Yahaya da yayi musamman a wannan lokaci da ake neman jajirtacce da ya kware a aikin soja domin kawo karshen hare-here da ake fama da su.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya sabon Babban Hafsan sojojin Najeriya
Janar Yahaya ya maye gurbin marigayi Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu a hadarin jirgi ranar Juma’a a Kaduna.
Darektan yada labarai na Ma’aikatar tsaron kasa,Onyema Nwachukwu.ya sanar da haka a wata takarda ranar Alhamis.
Manjo Janar Farouk Yahaya, dan asalin Karamar Hukumar Bodinga, Jihar Sokoto.
An haife shi ranar 5 ga watan Janairun 1966, a Sifawa.
Ya shiga aikin soja a 1985, kos na 37,a NDA.
Shine sabon Babban Hafsan sojojin Najeriya wanda shugaba Buhari ya nada ranar Alhamis.
Ya maye gurvin marigayi Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu a hadarin jirgin sama a Kadyna ranar Juma’a.
Allah ya taya shi riko. Amin
Discussion about this post