ZAFTARE MA’AIKATAN KADUNA: Zanga-zangar Ƙungiyar Kwadago ba zai yi tasiri a kan mu ba – Gwamnatin Kaduna

0

Gwamnatin Kaduna ƙarƙashin gwamna Nasir El-Rufai ta bayyana cewa babu abin da zanga-zangar Ƙungiyar Kwadago ya rage jihar da, cewa maganan zaftare ma’aikatan jihar nan na daram babu ja da baya akai.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin Jihar, Bara’atu Mohammed, ta bayyana haka a wata gajeruwar hira da ta yi da manema labarai a garin Kaduna.

” Wannan zanga-zanga da ƙungiyar Kwadago ta yi a Kaduna ba zai canja abinda gwamnati ta saka a gaba ba. Zaftare ma’aikatan jihar ne za mu yi ba za mu dakatar ba saboda haka su je can da boyayyar aniyar su ta siyasa da suka shigo da shi don su kawo rudani a jihar Kaduna.

” Mun gano cewa zanga-zanga ce aka shirya domin a gurgunta jihar, amma ba wai don a gyara wani abu da gwamnati ta yi da ba daidai ba.

” Duk da rudanin da zanga-zangar ya saka mutanen jihar, makarantu, asibitoci da ofisoshin gwamnati duk sun buɗe sun yi aiki yau.

” Su da kansu NLC sun sani cewa abinda suke yi ba zai hana mu ci gaba da abinda muka sa a gaba ba. Zaftare ma’aikata ne sai mun yi. Wai don sun yanke wutar lantarki zuwa garin Kaduna, sun rufe asibitoci, duk ba zai yi tasiri a kan mu ba. Muna nan akan bakar mu.

Kungiyar Kwadago ta bayyana cewa za ta ci gaba da zanga-zanga har sai ranar Juma’a mai zuwa kamar yadda ta tsara.

Su kuma mutanen Kaduna sun shiga cikin tsaka mai wuya musamman na rashin wutar lantarki a fadin jihar. Hakan ya yi matukar gurgunta harkokin kasuwanci da jin daɗin rayuwa a jihar.

Mutane na ganin tunda wannan saɓani zakanin gwamnati da ma’aikata me ya shafi dan kasuwa da mai wankin hula.

Share.

game da Author