Akwai tsarin mulki da yawa a duniya, an yi wasu a shekarun baya. Ana kan yin wasu a wannan lokacin. Saidai da yawansu sun zama kauyanci yanzu saboda shigowar tsarin mulkin dimokradiyya.
Manufar dimokradiyya, ita ce, ta ceto mutane daga mulki irin na tsohon mulkin kama-karya na gargajiya a wancan lokacin. Gwamnati wacce aka kafata da zabin al-umma don ta samar musu ‘yanci da cigaba sunanta dimokradiyya. Ko dalibin J.S 1 a secondary ya san wannan.
Gaskiya abun da yake faruwa a wasu jihohin a Najeriya ya sa6awa dimokradiyya. Musamman abun da yake faruwa a jihar Kaduna yanzu. A matsayinka na shugaban da aka zabeka, akwai hanyoyi da yawa da ake warware matsaloli a siyasa. Ai ita kanta siyasar, wasu suna bata ma’ana da: “tsari mai warware rikici da samar da zaman lafiya.”
Zama a tattauna (dialogue) yana da matikar amfani a siyasa. Kuma duk gwamnatin da bata damu da koke-koken mutane masu rinjaye ba, sunanta da turanci “public nuisance”
Korar mutane daga aiki ba karamin abu bane a gwamnatance. Gaskiya masifa ce ba karama ba. Musamman a kasar da ake cikin wani yanayi. Idan har kudi ake nema don tafiyar da gwamnati. Akwai abubuwa da yawa da basu kai korar ma’aikata illa ba.
Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya kalubalanci Gwamnatin Umaru Musa Yar Adua da ta Goodluck akan rashin samar da aikin yi da kuma albashi da alawus na yan siyasa. Yakamata ya saka gatari ya sare kudaden yan siyasar jiharsa don samun kudin yin ayyuka.
Allah ya shiryar da mu.