Za mu koya wa wadanda suka hargitsa Kaduna da sunan zanga-zanga darasin da baza su taba mantawa da shi ba – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce gwamnatunsa za ta maka wadanda suka yi zanga-zanga a Kaduna, domin sun karya doka ne.

” Idan muka koya musu hanakali, ba za su sake marmarin dawowa Kaduna ba su yi abinda suka yi ba.

El-Rufai ya fadi haka a wajen taron bunkasa tara Haraji da aka yi a dakin taro na Murtala Square, dake Kaduna.

Dakatar da yajin aiki

Shugaban kungiyar Kwadago ta Kasa, Ayuba Wabba ya bayyana cewa dalilin da ya sa kungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi a Kaduna shine domin bin umarnin kungiyar neman kungiyar da ma’aikatar kwadago ta yi mata na tazo a zauna domin samun mafita.

Wabba ya shaida wa manema labarai cewa saboda zamar da za ayi shine ya sa a kungiyar ta dakatar da yajin aikin.

Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da shugaban kungiyar NLC Ayuba Wabba su garzayo Abuja a tattauna domin a sasanta su.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin arangamar da aka yi ta yi tsakanin kungiyar Kwadago da gwamnatin Jihar Kaduna Tun daga ranar Litinin zuwa yau Laraba.

Gwamna El-Rufai ya lashi takobin ganin bayan kungiyar yana mai cewa ba zai janye daga shirin zaftare ma’aikatan jihar da gwamnati ke yi ba.

Haka ita ma kungiyar Kwadago ta ce ba za ta dakatar da Zanga-zangar ba har sai El-Rufai ya dakatar da zaftare ma’aikata.

Share.

game da Author