Wata likita dake fannin dai-daita jinsin maza da mata na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna Eugenia Akpa ta bayyana cewa wannan fanni na su zai hada hannu da karamar hukumar Kudan domin ganin mata sun ilmantu da ilimin Boko.
A watan Satumbar 2020 karamar hukumar Kudan ta kafa dokar samar da ilimin boko ga mata da ‘yan matan dake yankin.
“A dalilin haka ya sa za mu hada hannu da su domin ganin mata sun samu ingantacen ilimin boko a karamar hukumar.
“Za Kuma mu wayar da kan mutane musamman a makarantun sakandare game da illar dake tattare da cin zarafin mata da ‘yan mata.
Eugenia ta ce cin zarafin mata musamman fyade ya zama ruwan dare a jihar Kaduna sannan mafi yawan lokuta ba a iya hukunta masu aikata wannan aika-aika.
Ta ce rashin samun kwararran hujojjin da za su nuna cewa an yi wa mace fyade na daga cikin matsalolin dake hana a hukunta masu yi wa mata fyade koda an kama su.
Wannan kokari na jami’ar ABU zai taimaka matuka wajen kara ilmantar da mata a yankin da wasu matan na karkara.
Wasu da damu sun yaba wa wannan kokari na wannan fanni domin duba mata da su da kuma wayar musu da kai.
Discussion about this post