Yawan hare-hare kan ofisoshin INEC zai iya kawo wa zabukan 2023 cikas -Farfesa Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana damuwar sa dangane da yawan hare-haren da wasu batagari ke kai wa ofisoshin INEC a shiyyar kudu maso gabas.

A wani taron gaggawa da ya kira daukacin Kwamishinonin Zabe na jihohin Kasar nan, a Abuja, Yakubu ya ce yawan hare-haren banka wa ofisoshin zabe wuta da ake yi, zai iya kawo wa tsarin gudanar da zabukan 2023 cikas.

“Tabbas wadannan hare-hare na babu gaira babu dalili za su iya zama tarnaki ga dukkan kokarin da INEC ke yi tare da zubar da kimar tsarin zaben baki daya.”

Shugaban na INEC ya yi wannan kakkausan bayani ne biyo bayan banka wa wani ofishin INEC wuta da aka yi a jihar Ebonyi.

Harin na ranar Laraba dai shi ne hare-harena shida da aka kai wa ofisoshin INEC a jihohin Kudu maso Gabas.

Yakubu ya ce wannan hare-hare barnatar da dukiya ne, musamman a wannan hali da ake ciki na matsin tattalin arziki.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara maida himma wajen kare kadarorin gwamnati, musamman kadarorin da su ka shafi kayan zabe.

Ya sake yin kira ga jama’ar gari su zage damtse wajen bada kariya ga kadarorin da batagari ke kokarin lalatawa.

Harin baya-bayan nan dai shi ne wanda wadansu mutane da ba a san ko su waye ba, su ka banka wa ofisoshi uku na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) wuta a Jihar Ebonyi a ranar Laraba.

Ofisoshin su ne na kananan hukumomin Ezza ta Arewa da Izzi.

Jami’in Yada Labarai na INEC a jihar, Mista Cornelius Ali, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a Abakaliki, ya ce batagarin da su ka aikata hakan sun kone ofisoshin tare da injinan janareto da rumfunan zabe da wasu muhimman kayayyakin zabe.

Ya ce shugabannin hukumar sun kai ziyarar gani da ido zuwa ofisoshin da gobarar ta shafa da nufin sanin yawan barnar da aka yi.

Sai dai ya kwantar da hankali kan fargabar da ake yi kan ko wannan barna za ta kawo barazana ga shirin da ake yi na gudanar da aikin rajistar masu zabe wanda za a yi a watan Yuni.

Mista Ali ya ce, “A safiyar yau, mun samu rahoton cewa wasu mutane sun kai hari tare da banka wa ofisoshin mu na kananan hukumomin Ezza ta Arewa da kuma Izzi wuta, inda su ka lalata muhimman kadarorin hukumar.

“Da mu ka je can, mun ga an kone gine-ginen da ofisoshin mu din ke ciki yayin da kuma an ragargaza injinan janareto da rumfunan zabe da sauran kayayyakin INEC da ke cikin wadannan ofisoshin baki daya.”

Kakakin hukumar ya kara da cewa batagarin sun ja wa hukumar babbar asara, to amma ya ce harin ba zai rage mata kwarin gwiwa ba wajen sauke nauyin da aka dora mata na yi wa jama’a aiki.

Ita kuwa da aka tuntube ta, Jami’ar Yada Labarai ta Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ebonyi, Loveth Odah, cewa ta yi aiki ya yi mata yawa, ba za ta iya magana da ‘yan jarida ba.

Share.

game da Author