Yau ake muƙabala da malamin da ya ce ya auri Aljanna a Kano

0

Hukumomi a Kano sun tabbatar a yau Litinin za a yi Muƙabala da Malamin da ya ce ya auri Aljanna tun lokacin yana yaro.

Gidan Radio Express take Kano ta rawaito cewa Gwamnatin Kano, ƙarƙashin ma’aikatar addinai zata gabatar da titsiye ko Muƙabala da Malamin nan Dan asalin kofar Na’isa wanda yake da’awar ya auri aljana.

Wannan malami yace tun yana goye mahaifiyar sa ta faɗa dashi rijiya daga nan ne aljanu suka ɗauke shi suka ci gaba da shayar dashi, har ya girma.

Malamin ya ce yanzu haka ya auri aljana Umm Subyan ƴar sarkin aljanu har ta haifa masa’ ya’ya.

A saboda haka ne aka shirya zama da wannan malamin aljanu domin rarrabewa da baccin makaho.

Share.

game da Author