‘Yan sandan Kano sun damke matashin dake like bakin ATM, daga baya ya cire kudaden mutane da suka ki fitowa

0

Darektan hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya bayyana yadda jami’an ‘yan sandan Kano suka kama wani matsahi dan shekara 22 da ke satar kudin mutane a ATM ta hanyar yin wata dabara.

ASP Kiyawa yace kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Samaila Dikko, ya umarci jami’an ‘yan sandan su fantsama neman wanna matashi inda suka yi sa’an kama shi a daidai yana aikata abin a banki.

Matashin mai suna Bashir Bala, ya ce ” Na kan je ATM kamar zan cire kudi, idan na tsaya jikin ATM din sai in saka wani roba da abin like kudi wato ‘salatep’ sai in manne shi ta yadda kudi ba zai fito ba. Sai in ja gefe kamar ina yin wani abin. Idan mutum ya zo ya saka katin sa, ita naurar ATM din za ta kirga kudin amma saboda na toshe bakin ta sai ba zai fito ba.

BIDIYO: YADDA ‘YAN SANDAN KANO SUKA DAMKE BARAWON KUDIN MUTANE A ATM – ASP Abdullahi Kiyawa

” Yan barin wajen sai in koma kamar zan cire kudi zai in zare robar da na saka sai in dinga zakulo kudaden da suka makale.

Kiyawa ya tambayeshi zuwa yanzu ya sace ya kai nawa, inda ya ce masa ya sace kudi sun kai naira 300,000.

” Ni dan Gombe ne amma bana yi a Gombe saboda an sanni sosai, kuma ATM din su ba irin bakin da ake toshewa bane.

Share.

game da Author