‘Yan sanda sun ceto masallata 30 cikin mutum 40 da mahara suka sace a Katsina

0

Kakakin rundunar’ Yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya bayyana cewa, ‘Yan sanda da’ Yan banga sun ceto masallata 30 cikin 40 din da aka sace a Jibia, jihar Katsina.

Isah ya bayyana wa BBC Hausa cewa jami’an ‘Yan sanda da’ Yan banga sun bi sawun wadannan ‘yan bangan inda suka yi nasarar ceto masallata 30.

“Sai dai akwi wasu mutum 10 da ba a gansu ba har yanzu. Ana dai ana ci gaba da bincike.

An Kwashi Mutum 18 Da Rana Tsaka A Garin Tsaskiya:

Rahotanni da wasu kafafen yada labarai a Katsina sun tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa a ranar Asabar ‘yan bindiga sun yi wa garin Tsaskiya tattaki wajen 12 na rana, su ka hargitsa garin da harbe-harben bindiga, kuma su ka kwashi mutum 18, su ka nausa cikin daji da su.

Garin Tsaskiya ya na yammacin garin Dutsinma, amma ya na karkashin Karamar Hukumar Safana.

PREMIUM TIMES HAUSA ta zanta da wani mutumin Dutsinma mai suna Jamilu Ibrahim wanda ya tabbatar da cewa da idon sa ya ga abin tausayi.

“Na ga yadda mutanen garin Tsaskiya ke tururuwa, sun tako kasa zuwa nan cikin garin Dutsinma domin gudun tsira da rayukan su.

“Ina tabbatar maka kuma har yau gwamnatin Jihar Katsina ba yi magana kan mutanen da aka kwasa su 18 a Tsaskiya ba.” Inji shi.

Lokacin rubuta wannan labari dai Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ba ta yi magana ba, amma majiyoyi a Katsina sun ce jami’an tsaro na cewa masallata 11 kawai aka gudu da su a Jibiya.

Share.

game da Author