‘Yan sanda da’ Yan banga sun kashe mahara 10 Zamfara

0

‘Yan sanda da’ Yan banga sun kashe mahara 10 a kauyen Hayin Daudu, dake Gusau ranar Litinin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammed Shehu ya bayyana wa manema labarai cewa wasu’ ‘yan garin ne suka kwada wa’ yan sanda waya cewa mahara sun shigo musu gari suna ta harbe harbe.

Daga nan ne fa da mu jami’an yan sanda da yan banga muka fantsama zuwa wannan gari na Hayin Daudu.

” Ko da muka isa wannan gari sai muka iske ‘yan bindigan dauke da manyan bindigogi, daga nan ne muka fantsama batakashi da maharan har Allah ya bamu sa’ an kashe mutum 10 daga cikin su sannan wasu da dama suka arce da rauni a jikin su.”

A karshe jami’an yan sanda da yan banga basu fice daga garin ba sai da suka tabbatar zaman lafiya ya dawo cikin garin.

Share.

game da Author