Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna, sun ki sakin su saboda ‘yan bindigar na da alaka da Boko Haram.
Gumi ya yi wannan furuci a wata hira da ya yi da Channels Television a ranar Lahadi, a Kaduna.
‘Yan bindigar dai sun saci dalibai 20 daga Jami’ar Green Field, wadda ke kan titin Kaduna zuwa Abuja a ranar 17 Ga Afrilu, kuma zuwa yanzu sun kashe biyar daga cikin su.
Sun kuma yi barazanar kashe sauran idan ba a biya su diyyar naira miliyan 100 ba kafin su sake su.
A hira da Gumi ya ce ba kamar garkuwar da ake yi da mutane a yankin Arewa maso Gabas ko Arewa maso Yamma ba, “su wadanda zu ka sa ci daliban su na da alaka da Boko Haram a cikin dajin.
“Wannan ne karon farko a garkuwa da mutane inda mu ka tabbatar da alaka tsakanin ‘yan bindiga da Boko Haram. Hakan ya nuna yadda Boko Haram ke kara kutsowa, kuma hakan gagarimar matsala ce.” Inji Sheikh Gumi.
Gumi ya kara da cewa ‘yan Boko Haram sai da su ka tuntubi ‘yan bindigar da su ka saci daruruwan dalibai a sakandaren Kankara ta Jihar Katsina, har su ka nemi su sayar masu da dukkan daliban, domin sun tabbatar za su dubanya riba a wurin tattauna sakin su.
Sai dai Gumi ya ce ‘yan bindigar ba su amince da tayin da Boko Haram su ka yi masu ba. Sun saki dukkan daliban bayan sun cimma sasantawa tsakinin su da Gwamna Matawale na Zamfafa.
“To amma tattauna sakin sauran daliban Greenfield University abu ne mai wuyar sha’ani, saboda alakar ‘yan bindigar da Boko Haram.” Cewar Gumi.
Discussion about this post