‘Yan BINDIGA: ‘Yan sanda biyu sun rasu, mahara da dama sun sheka lahira a Zamfara

0

Kakakin rundunar’ Yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an ‘Yan sanda biyu sun rasu a batakashi da yan sanda suka yi da gungun mahara a Magami, karamar hukumar Gusau.

Muhammed ya ce yan sandan sun kai wa mutanen Magami dauki ne bayan an sanar da su cewa wasu gungun mahara sun afka garin bisa babura.

” Ko da jami’an ‘yan sanda suka isa garin Magami sai aka fara dauki ba dadi a tsakanin su da maharan.’ Yan sanda sun yi nasarar kashe mahara da dama, sannan wasunsu sun arce da rauni a jikin su.

Mohammed ya ce, sai dai kuma suma ‘Yan sandan sun rasa jami’ ai biyu.

A karshe dai ya ce, kwamishinan ‘Yan sandan jihar ya aika da karin jami’ ai a wannan yanmi domin samar da tsaro gudun kada maharan su sake dawowa.

Share.

game da Author