‘Yan bindiga sun sace shugaban Miyetti Allah

0

Wasu’ Yan bindiga sun sace shugaban Miyetti na jihar Kogi Wakili Damina a gidansa dake Chikiri, karamar Hukumar Kogi.

Sakataren kungiyar, Adamu Abubakar ya bayyana wa manema labarai a garin Lokoja cewa maharan su takwas sun zo gidan Damina da karfe 12 na rana, a wata mota kirar Bus suka saka shi cikin ta da karfin tsiya.

Adamu ya ce kanin Damina da aka yi abin a idon sa ya shaida masa abinda ya faru.

Har yanzu maharan ba su ce komai ba tukunna game da ko suna bukatar kudin fansa, da kuma ko nawa suka saka farashi.

Rundunar ƴan sandan jihar sunce har yanzu ba a kawo karar sace Damina a ofishin ta ba.

Share.

game da Author