Barayin shanu sun bindige Sardaunan Kwantagora, Bashir Namaska, ranar Alhamis a Gandun Sarki.
Bashir Namaska wanda shi ne mai rike da sarautar Sardaunan Kwantagora, an bindige shi a gandun Sarki, a lokacin da ‘yan bindigar su ka kai hari tare da sace shanun da ke cikin gandun.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Usman ya tanbbatar da cewa Sardaunan Kwantagora ya rasu a hanyar zuwa Asibitin Kwantagora, sakamakon harbin bindigar da aka yi masa a kafadar sa ta hagu.
Jihar Neja ta shiga sahun jihohin da matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da satar dabbobi su ka addaba.
Haka nan Karamar Hukumar Kwantagora na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane ana garkuwa da su.
Makonni uku da su ka gabata Gwamna Sani Bello ya bayyana cewa Boko Haram sun kafa sansani cikin wani kauye a Karamar Hukumar Shiroro.
Sai dai kuma kwanan nan Gwamnatin Jihar ta tabbatar da cewa al’ummomin yankuna 20 da su ka yi gudun hijira na ci gaba da komawa kauyukan su.
Ko cikin makon da ya gabata, sai da Gwaman Jihar Neja Sani Bello ya sanar cewa ‘yan bindiga sun bindige sojoji uku a Jihar Neja.
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Bello ya bayyana cewa cewa ‘yan bindiga sun kashe sojoji uku a Karamar Hukumar Magama.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Bello ya ce su ma sojojin sun kashe ‘yan bindiga da dama, sun kuma dauko gawarwaki biyu na ‘yan bindigar.
Kakakin Yada Labarai ta Gwamnan Neja, Mary Noel-Berge ta kara jaddada haka cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan taron da gwamnan ya yi da Shugabannin FannoninTsaro na Jihar Neja a Gidan Gwamnatin Jihar.
Sannan kuma ya ce sauki ya fara samuwa, domin yankuna 25 da ‘yan bindiga su ka tilasta wa yin gudun hijira duk sun koma garuruwan su.
“A yanzu haka jama’a na ci gaba da barin sansanonin gudun hijira su na komawa gidajen su a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Mariga.
“Amma har yanzu ana samun ci gaba da zaman zullumi a wasu yankunan.”
Daga nan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara kaimin kai jami’an tsaro.
Cikin watan jiya ne Gwamnan Jihar Neja ya bayyana cewa Boko Haram sun kama wani kauye a jihar Neja har jama’ar kauyen sama da 2000 sun tsere.
An kashe sojojin kwana biyu bayan PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin bindige mutum 723, tare da yin garkuwa da mutum 407 cikin watan Afrilu a Najeriya.
Kungiyar Nigeria Mourns, mai bin diddigin asarar rayuka a yake-yake da rikice-rikice a cikin Najeriya, ta bayyana cewa a cikin watan Afrilu 2021, akalla an kashe mutum 723, kuma aka sace mutum 407 aka yi garkuwa da su.
Daga cikin wadanda aka kashe din dai 500 duk fararen hula ne, saura 133 kuma jami’an tsaro ne daga bangadorin tsaro daban-daban.
‘Yan bindiga ne su ka kashe mutum 426, yayin da Boko Haram su ka kashe mutum 117. Sauran wadanda su ka rage a adadin lissafin wasu sun mutum a hannun jami’an tsaro, wasu a rikicin ‘yan kungiyar asiri, wasu kuma wurin rikicin kabilanci.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka kashe mutum 1,603, an sace mutum 1,774 a Najeriya.
A cikin rahoton, akalla an samu tabbacin kashe mutum 1,603 a hare-hare daban-daban a fadin kasar nan, tsakanin watan Janairu zuwa Maris, 2021.
Wata kungiya ce mai suna Nigeria Mourns ta tabbatar da wannan kididdigar.
Rahoton na “Munanan Hare-haren Cikin Janairu zuwa Maris 2021″, sun wallafa shi a ranar Lahadi.
Nigeria Mourns ta ce ta tattaro adadin wadanda ta ce an kashe din daga rahotannin da jaridu su ka buga, sai kuma jawaban da dangin wadanda aka kashe din su ka furta.
Sannan kuma rahoton ya nuna an yi garkuwa da mutum 1,774 a cikin watan Janairu zuwa Maris a fadin kasar nan.
Rahoton ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 921, Boko Haram ko ISWAP sun kashe mutum 207, wasu mutum 205 kuma a daidaikun hare-haren nan da can aka kashe su. Sai kuma wadansu mutum 106 da rahoton ya ce a rikice-rikicen ‘yan kungiyar asiri aka kashe su.
Kisan-gillar da jami’an tsaro ke yi ba tare da hukunta mai laifi ba ya haddasa kisan mutum 79 a hannun jami’an tsaro, rikice-rikicen kabilanci ya ci rayuka 53, yayin da makiyaya su ka kashe mutum 32.
Daya daga cikin ‘yan kungiyar Nigeria Mourns mai suna Ier Jonathan, ya ce kashe-kashen ya yi muni matuka, amma ba an fito da adadin ba ne don a ci mutuncin gwamnati.”
Yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar nan, abin ya kai ga rahotannin bayyanar Boko Haram a wasu jihohin da su ka hada Nasarawa, Bauchi, Neja da kuma alakanta masu garkuwar da su ka sace dalibai 20 na Jami’ar Greenfield ta Kaduna, su kuma gwamnoni 17 na kudancin kasar nan, sun bijiro da wasu matakan tsaron da ake ganin kamar fito-na-fito ko nuna gazawar gwamnatin Buhari ce su ka yi kuru-kuru.
“Shaidanun Mutane Masu Kambun-baka Ne Su Ka Tasa Gwamnatin Buhari A Gaba” -Femi Adesina”
Kakakin Yada Labaran Shugaba Muhammadu Buhadi, wato Femi Adesina, ya bayyana cewa shaidanun mutane masu kambun-baka, wadanda ya kira Aeye da Ysrabanci ne su ka tasa gwamnatin Buhari a gaba.
Ya ce dalili kenan ba a ganin namijin kokarin manyan ayyukan raya kasar da Buhari ke yi, sai matsalolin da ke damun kasar nan su ka fi fitowa fili.
“Idan ka na kakari ka na aikata ayyuka muhimmai a kasa, za a samu wasu shaidanun mutane masu kambun-baka, wadanda ba su ganin alherin sa, kuma ba su yayata alheri sai sharri. To irin wadannan da Yarabawa ke kira Aeye, idan su ka ta sa ka a gaba, duk da irin kokarin da ka ke yi, to za a rika cin karo da ibtila’in da ka na kokari amma wani abu na shantale maka kafafu. Ka na binne shuka, bayan ka tashi daga gona, ka tafi gida, sai shaidanu masu kamdbun-baka su rika bi su na tonewa.” Inji Adesina, a cikin wani rubutun sa da ya fitar ranar Alhamis.