‘Yan bindiga sun afka garin Madalla, sun kashe mutum daya sun sace mutum 12

0

Wani mazaunin garin Madalla dake Abuja, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kawo hari garin Madalla sun kashe wani mutum daya kuma sun arce da mutane 12.

” Mahara sun kai su 30 da suka kawo harin. Wannan shine gaskiyar magana. Sun Kashe wani mutum daya sannan sun arce da mutane 12.
Wannan shine karon farko da irin haka zai auku a wannan gari na mu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Abiodun Wasiu, ya bayyana cewa har yanzu rundunar ba ta samu ainihin yawan mutanen da ta aka sace ba sai dai tana nan tana ci gaba da bincike akai.

Jihar Neja na cikin jihohin Arewa da matsalar rashin tsaro yayi tsanani a kasar nan. Boko haram sun kwace karfin Iko a wasu kananan hukumomi biyu a jihar.

Bayan haka sun aure matan garin gaba daya ga mayakan su sannan sun kakkafa tutoci.

Gwamnan jihar ya ce ya gaji da jin ga kaho nan baiga shanu ba daga gwamnatin tarayya. Ya ce rashin tsaro ya addabi mutanen jihar amma kuma gwamnatin tarayya ba ta yi komai ba a kai.

Jihohin Katsin, Kaduna, da jihar Neja na fama da tsanin rashin tsaro a kasar nan.

har yanzu akwai daliban jami’ar Greenlanda jihar Kaduna dake tsare a hannu Boko Haram ba a sako su ba.

Share.

game da Author