Yadda ‘yan sanda su damke mutumin da ya sace dan makwaucin sa ya kashe shi bayan ya karbi kudin fansa

0

Rundunar’ Yan sandan Kaduna ta kama wasu matasa uku da mace daya da suka yi garkuwa da wani yaron makaucin gogarman wanda ya jagoranci garkuwa da yaron dan shekara 6 a unguwar Badarawa dake Kaduna.

Shi dai wannan yaro makaucin su ne a sace shi ya mika wa gogarman su arce da shi Kano.

Daga baya suka nemi mahaifin ya biya kudin fansa naira miliyan 1.

Maimakon su maido masa da yaron sai daya daga cikin su ya ce yaron ya gane su fa kuma zai iya tona musu asiri idan ba su dau mataki ba.

Daga nan sai suka yanke shawarar su kashe yaron kawai su ja bakin su su yi shiru.

Daga nan sai suka murde kan wannan yaro suka kashe shi suka kuma jefa shi kwararo suka kama gaban su.

Mohammed Jalinge, Kakakin ‘Yan sandan Kaduna ya shaida wa manema labari cewa rundunar na ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke aiki da wadannan masu garkuwa da mutane.

Share.

game da Author