Yadda ‘yan bindiga suka sace shanu 300, suka farfasa shagunan mutane da rana tsaka a Dansadau

0

‘Yan bindiga dauke da bindigogi sun sace shanu 300 da kayan shagunan mutane a garin Dansadau dake karamar hukumar Maru jihar Zamfara.

Majiya ta bayyana cewa maharan sun afka wa kauyen ne da karfe 4 na yammacin Talata.

Maharan sun shigo kauyen bisa babura su 150 a wannan rana, sannan sai da suka dauki tsawon awa biyu suna cin karen su ba babbaka a kauyen.

Wannan abin tashin hankali ya auku ne mako daya bayan wasu mahara sun shiga kauyen Samawa Bungudu dake karamar hukumar Bungudu jihar Zamfara.

Maharan sun banka wa gidajen mutane wuta wanda a dalilin haka mazauna kauyen sun zama ‘yan gudun hijira na karfi da yaji.

Share.

game da Author